Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati
- Babu abin da ke jawo wadanda ke aikin gwamnati suyi sata irin tsoron halin da za su shiga bayan ritaya
- Dr. Goodluck Jonathan yana ganin a dalilin wannan, ma’aikata suke saba doka domin su tanadi dukiya
- Jonathan ya soki yadda dokokin Gwamnati suka haramtawa ma’aikatan gwamnatin yin kasuwanci
Abuja – A makon nan Goodluck Jonathan yace tsoron abin da zai faru da rayuwarsu bayan sun yi ritaya, shi yake jawo ma’aikatan gwamnati suyi sata.
Vanguard tace Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan jawabi ne da yake bayani a wajen kaddamar da wani littafi da Obioma Onwuzurumba ya rubuta.
Onwuzurumba wanda ya yi aiki a matsayin Fasto a fadar shugaban kasa ya rubuta littafi wanda aka kaddamar a ranar da ya cika shekaru 73 a Duniya.
An kira tsohon shugaban kasar ya gabatar da jawabi na musamman a ranar, a nan ne ya tattauna a kan rashin gaskiyar da ma’aikatan gwamnati suke yi.
Ya makoma za ta kare?
"Daga cikin manyan matsalolin da muke da su a Najeriya, kuma watakila yake jawo ake rashin gaskiya sosai shi ne rashin sanin yadda gobe za ta kasance.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Saboda haka sai mutane su ce tun da yanzu ina aiki, bari in taimaki kai na ta muguwar hanya."
- Dr. Goodluck Jonathan
Jonathan ya yabawa Obioma Onwuzurumba
Tribune tace Dr. Jonathan ya ji dadin ganin yadda Onwuzurumba da mai dakinsa suka kafa cibiyar da za ta rika kula da tsofaffin mutanen cikin al’umma.
A jawabinsa, tsohon shugaban na Najeriya ya kuma koka a kan yadda dokar kasa take hana ma’aikatan gwamnati yin kasuwanci a lokacin da suke aiki.
"Baya ga haramta masu yin kasuwanci, idan ma’aikatan sun yi ritaya, ba a kula da su sosai.
Babu wani tsarin kula da walwalar al’umma. Musamman idan ka duba mutanen da ke aikin tsaro, misali a yau na saurari wata hira a gidan rediyo.
Kuma dokokinmu ba su barin ma’aikatan gwamnati su kafa kamfani, illa noma. An hana ka kasuwanci da ka na aiki, ka gama aiki, ba a kula da kai."
- Dr. Goodluck Jonathan
Rahoton yace Farfesa Jerry Gana ya yi jawabi a wajen taron, shi ma ya koka da cewa yanzu mutanen da ake da su masu gaskiya da mutuncin sun yi karanci.
Sanata Anyim Pius Anyim, Ama Pepple da Fastoci irinsu Henry Ndukuba da Archbishop Peter Akinola sun zo wajen bikin kaddamar da wannan littafi.
Ina da kudi, ba zan musanya arziki na ba - Tinubu
A jiya ne aka samu labari cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amsa zargin da ake yi masa na samun dukiya ta hanyar yin sata da kuma taba baitul-malin Legas.
‘Dan takarar na APC yace babu hujjar da ke nuna ya ci kudin gwamnati, yace a sanadiyyar hannun jari da gado ya zama Attajiri har ‘yan adawa suke hassada.
Asali: Legit.ng