Sojojin Najeriya Sun Kashe ’Yan Bindiga da Dama a Wasu Manyan Dazukan Jihar Kaduna

Sojojin Najeriya Sun Kashe ’Yan Bindiga da Dama a Wasu Manyan Dazukan Jihar Kaduna

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe tarin 'yan ta'adda a wasu manyan dazuka uku na jihar Kaduna a Arewa masu Yammacin kasar
  • Kwamishina a jihar Kaduna ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda yace an kuma raunata 'yan bindiga da dama da suka tsere
  • Hukumomin tsaron kasar nan na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a kwanakin nan, musamman yayin da ake tunkarar zaben 2023

Jihar Kaduna - Jami’an sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga a wani aikin kakkabe ‘yan ta’adda a dazaukan Isasu, Fatika da Makera da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Punch ta ruwairo.

Ya bayyana cewa, bisa bayanai daga sojojin, an hallaka ‘yan bindiga da daa yayin da aka jikkata wasu da suka tsere da raunukan harbin bindiga zuwa jihohin makwabta.

Kara karanta wannan

Buhari da Magashi Suna Cikin Sokoto, ‘Yan Bindiga Sun Sheke ‘Yan Sanda 3 da ‘Yan Kasuwa 3

Kwamishinan ya nemi goyon bayan jama’ar yankin, inda ya nemi su ba da rahoton duk wani da suke zargi da ya zo neman magani matukar aka ganshi da harbin bindiga.

Bayan da kwamishinan ya yi

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A cewar rahoton, an tabbatar da kashe ‘yan bindiga da dama ya zuwa yanzu, yayin da wasu kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga zuwayankin Hayin Sidi da ke makwabtaka da jihar.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta karbi rahoton tare da yaba aikin sojoji bisa samun wannan nasarar, yayin da take bukatar su kara kaimi a aikinsu.”

Gwamnati ta ba da lambar wayan da za a kira duk sadda aka ji motsin wasu tsageru ko kuma ‘yan bindigan da suka zo neman magani cikin al’umma.

Ga lambobin da za a kira domin ba da rahoton motsin 'yan bindiga, kamar yadda Within Nigeria ta tattaro: 09034000060 and 08170189999.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Borno

A wani labarin kuma, an samu tsaiko a jihar Borno yayin da makiyaya da manoma suka kaure da fada, an hallaka mutane takwas tare da raunata wasu.

Hakazalika, rahoton da muka samo ya bayyana cewa, an kone gidaje 47 kurmus a wannan mummunan fada da ya ya tashi.

Hukumomin tsaro da kungiyoyi sun taru domin dinke barakar da kuma kare faruwar irin wannan barnar a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.