Budurwa Ta Tunkari Magidanci Ta Nemi Lambar Waya a Gaban Matarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

Budurwa Ta Tunkari Magidanci Ta Nemi Lambar Waya a Gaban Matarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wani Bidiyon barkwanci dake yawo a Soshiyal Midiya ya nuna yadda wata budurwa mai diri taje gaban wani Mutumi yana tare da matarsa
  • A gaban gidan Abinci, budurwar ta kyalla ido ta ga ma'auratan biyu nan take ta yanke taka wasan tsokana da su
  • Bidiyon ya nuna yadda ta je har gaban mutumin kana ta nemi ya bata lambarsa yayin da matarsa da sauran mutane suka shiga mamaki

Wani mawallafi a soshiyal Midiya, King_Mitchy ya taba wasan barkwanci da wasu ma'aurata a wurin cin abinci.

A wani bidiyo, wata budurwa ta je har gaban ma'auratan kana ta fara zuba kalaman yadda ta yi sha'awar mutumin daga ganinsa.

Wasan barkwanci.
Budurwa Ta Tunkari Magidanci Ta Nemi Lambar Waya a Gaban Matarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: King Mitchy
Asali: UGC

Ba tare da bata lokaci ba, dirarriyar budurwan ta nemi ya ba ta lambar wayarsa a gaban mai ɗakinsa, matar ta ɗaga ido ta kalleta cikin mamaki da kaɗuwa.

Kara karanta wannan

Kwana Huɗu da Aure, Amarya Ta Kama Ango Na Saduwa da Yar Uwarta a Gado, Ta Turo Bidiyo

"Ka haɗu, dan Allah zan iya samun lambar wayanka?" Budurwar ta tambayi mutumin a gaban matarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da zai bata amsa, mutumin ya waiwaye matarsa sannan ya nemi ta karanta wa budurwar lambarsa, cikin ɗacin rai matar ta ƙi yarda sam. Tace ba ta yadda ba.

Sai dai daga ƙarshen Bidoyon mawallafin ya bayyana cewa wasan barkwanci ne kawai aka shirya wa ma'auratan.

Kalli bidiyon anan

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani

@mhizp80 tace:

"Da ni ce a matsayin wannan matar auren, har na fara tausaya wa budurwan nan. Kina abu kamar wacce ta fito daga kauye hmmm."

@olayinkaika ya ce:

"Kar ta yi wannan wasan barkwancin da wani wanda ke cikin matsala ko wanda bai jima da farfaɗowa ba saboda akwai yuwuwar batun zai canza."

@timxtimgh ya ce:

"Yanzu ace matar aure na can gida tana kallon mijinta na cin amanarta da Sakatariyar Ofis sai kuma ga wata sabuwa ta danno kai, Baba kai babba ne."

Kara karanta wannan

Sharrin GB Whatsapp: Matashi Ya Gano Budurwarsa Na Yi Masa Yankan Baya, Ya Fallasa Ta

A wani labarin kuma Wata mata ta nuna farin ciki da jin daɗinta yayin da ta kama ɗanta kwance yana bacci tare da mai aikinta a gado

Matashiyar matar wacce ta yi ikirarin cewa har yanzun bata kai ga yin aure ba, tace tana rayuwa ne da ɗan da Allah ya bata sai kuma matar dake musu aiki.

Ta nuna matuƙar jin daɗinta ganin yadɗa yar aikin ta zama tamkar yar uwarta ta yadɗa take kula mata da karamin ɗanta, mutane sun maida martani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel