Kyawawan Hotunan Auren Wata Budurwa Yar Najeriya Da Angonta, Sun Hadu Ne A Facebook
- Wata budurwa yar Najeriya ta yi murnar aurenta da hadadden saurayin da ta hadu da shi a dandalin sadarwa na Facebook
- Ta shawarci yan mata da su dunga amsa sakonninsu, tana mai cewa akwai mazajen kwarai a dandalin Facebook
- Duru Chukwu Amaka Providence ta cika da mamakin yadda suka tashi daga abokai a Facebook zuwa abokan rayuwa
Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Duru Chukwu Amaka Providence ta auri sahibinta da ta hadu da shi a dandalin sadarwa na Facebook.
Amaka wacce ta cika d farin ciki ta je dandalin Rant HQ Extention a Facebook don bayar da labarin mai dadi tare da wallafa hotunan shagalin bikinta.
Amaka na da sako zuwa ga yan mata
Sabuwar amaryar ta bukaci yan mata da su dunga amsa sakonnin da ake aika masu sosai, tana mai cewa akwai mazajen kwarai sosai a dandalin Facebook.
Yadda Dangin Mijina Suka Umurci Ɗayansu Ya Gaje Ni Bayan Rasuwarsa, In Ji Matar Yar Jihar Arewacin Najeriya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta cika da shauki kan yadda abokinta na Facebook ya zama abokin rayuwarta a yanzu. Wallafan nata ya zo kamar haka:
"Mazajen aure sun cika Facebook ku yi kokari ku dunga amsa sakonninku.
"Na hadu da mijina a Facebook mun tashi daga abokan Facebook zuwa abokan rayuwa.
"Dan Allah ku tayani murna na fita daga layin yan mata."
Jama'a sun yi martani
Queen Zara Zara ta ce:
"Mazajen Facebook dinnan koooo wallahi idan kika hadu da daya.
"Za ki ji dadin hakan sun fi dadin sha'ani.
"Kirki, biyayya suna da zuciyar kyauta.
"Na tayaki murna yarinya."
Nancy Nwagboso ta ce:
"Na tayaki murna yar'uwa.
"Amma kada ki bari sauran mutane su dunga ba duk wanda ya tura masu sako hankalinsu.
"Wasu kawai suna neman wanda zasu yi amfani da ita ne yar uwa Disamba muke ciki faaa."
Auren mata da yawa: Jigon PDP ya bukaci mazan kudu da su yi koyi da na arewa
A wani labarin kuma, attajirin dan Najeriya kuma dan takarar kujerar sanata a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Ned Nwoko ya kalubalanci mazan kudancin Najeriya da su yi koyi da mazan arewa wajen auren mata barkatai domin rage yawan karuwai a yankin.
Nwoko ya yi ikirarin cewa rashin auren mata da yawa ne yasa karuwai suka yawaita a yankin domin samun na kashewa daga mazan aure masu mace daya a gida.
Asali: Legit.ng