Jigon PDP Ya Caccaki Mazan Kudu Kan Tara Yan Mata, Ya Nemi A Fara Auren Mata Da Yawa Don Hana Karuwanci

Jigon PDP Ya Caccaki Mazan Kudu Kan Tara Yan Mata, Ya Nemi A Fara Auren Mata Da Yawa Don Hana Karuwanci

  • Ned Nwoko, dan takarar kujerar sanata a yankin Delta ta arewa a PDP, ya ce mazan kudu ne suka sa karuwanci ya yawaita a yankin
  • Nwoko, wanda ke auren jarumar fim da wasu mata uku, ya ce idan da mazan kudu na auren mata fiye da daya kamar takwarorinsu na arewa, da mata da dama basu shiga karuwanci ba
  • Dan siyasar mai yara 19 ya jaddada cewa shi da babban basaraken kasar Yarbawa, Ooni na Ife, suna taimakawa al'umma ne ta hanyar auren mata da yawa

Ned Nwoko, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma mijin jarumar Nollywood, Regina Daniels, ya ga laifin mazan kudancin kasar kan yawan karuwai da ake samu a yankin.

Nwoko wanda ke neman takarar tikitin sanata mai wakiltan Delta ta arewa a PDP, ya ga laifin mazan kudancin Najeriya kan karfafa karuwanci a yankin ta hanyar guje ma auren mace fiye da daya, jaridar The Guardian ta rahoto.

Ned Nwoko
Jigon PDP Ya Caccaki Mazan Kudu Kan Tara Yan Mata, Ya Nemi A Fara Auren Mata Da Yawa Don Hana Karuwanci Hoto: Ned Nwoko foundation
Asali: Twitter

Jigon PDP Ned Nwoko ya soki mazan kudancin Najeriya kan guje ma auren mata da yawa

Jigon na PDP ya nuna takaicinsa kan yadda mata da dama suka zabi karuwanci a matsayin sana'a saboda maza da dama a kudancin Najeriya sun ki yin koyi da takwarorinsu na arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar mijin Regina Daniels:

"Mutumin kudu na iya kasancewa da mata daya, amma kuma yana da yan mata da yawa, sannan yana kashe kudadensa kan yan mata, wasu lokutan ma fiye da yadda yake kashewa matarsa ta sunnah."

Dan siyasan haifaffen Delta ta bayyana cewa idan namiji ya auri mata fiye da daya, zai mayar da hankali kan matan da yaransa.

Nwoko ya ce maza masu mata da yawa suna kashe kudadensu ne a kan iyalinsu kuma da wuya ka gansu da yan mata, sabanin yadda masu karuwai da dama a waje ke kashewa.

Mijin mace hudu da yara 19 ya ce shi da Ooni na Ife suna taimakawa al'umma ne kamar yadda suke ta kara auren mata, rahoton PM News.

Saurayi ya gano budurwarsa na cin amanarsa da wani ta GB Whatsapp, ya shata layi a tsakaninsu

A wani labari na daban, mun ji cewa GB Whatsapp ya yi sanadiyar rabuwar wani saurayi da budurwar da yake kauna.

Saurayin dai ya gano cewa budurwar na cin amanarsa da taimakon wannan dandali na sadarwa bayan ta aika masa wani sako bisa kuskure, ta goge sakon amma ya bankado shi da taimakon GB Whatsapp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel