Abin da Ya Sa Ba Zan Yarda a Kwantar da ni a Asibitin Gida ba – Atiku Abubakar
- Atiku Abubakar ya bayyana abin da ya sa ba zai yarda a duba shi idan bai da lafiya a asibitin Najeriya ba
- ‘Dan takarar shugaban kasar yana ganin akwai wasu bangarorin da aka yi wa likitocin kasar nan nisa
- Atiku mai neman mulki a 2023 a jam’iyyar PDP ya yi ikirarin cewa ya na da cikakkiyar koshin lafiya
Lagos - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ki daukar alkawarin amfani da asibitocin Najeriya idan ya karbi mulki.
Jaridar Premium Times tace an bijirowa Alhaji Atiku Abubakar tambaya game da sha’anin kiwon lafiya a lokacin da aka zanta da ‘yan takaran 2023.
Da aka yi masa maganar yin amfani da asibitocin Najeriya domin jinya ko da rashin lafiya ta kama shi, ‘dan takaran ya nuna ba zai zauna a kasar ba.
“Inda za a kula da lafiya ta?...Ba zan yi ba, akwai abin da ya fi karfinmu.” - Atiku Abubakar
Rahoton yace ‘dan siyasar ya tabbatar da cewa zai fito da bayanin lafiyarsa domin ya gamsar da mutanen Najeriya cewa yana cikin koshin lafiya.
Atiku ya halarci taron tare da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso masu takara a LP da NNPP, a nan aka ji yace gwamnati ba ta warewa harkar lafiya kudi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A asibitocinmu za mu zauna - Obi, Kwankwaso
Da aka zo kan Rabiu Kwankwaso, ‘dan takaran ya bayyana cewa zai yi amfani da asibitocin da ake da su a Najeriya idan yana bukatar ganin Likita.
“A kan zuwa ketare neman magani, akwai bukatar muyi abubuwa biyu. Na farko mu gyara abubuwan da muke da su; ta hanyar inganta asibitocin gwamnati.
Na biyu, mu karfafawa ‘yan kasuwa su shigo cikin harkar. Sannan ana bukatar shugabanni su zama abin misali, su kwanta a asibitocinmu na gida.”
Tsohon gwamnan na Kano yace dole mai neman shugabancin al’umma ya fadi gaskiyar halin lafiyarsa, yace shi zai iya kawo shaidar da ke nuna garau yake.
Shi ma Peter Obi ya shaidawa jama’a cewa har gobe yana amfani da asibitocin da ya gina a jihar Anambra ne a lokacin da ya yi mulki tsakanin 2006 da 2014.
Matsalar Gwamnoni - Atiku
An samu rahoto ‘Dan takaran Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya gaskata abin da Mai girma Muhammadu Buhari ya fada a kan Gwamnoni.
Atiku Abubakar ya bada labarin irin takaddamar da suka fuskanta da Gwamnoni bayan sun yi yunkurin ba kananan hukumomi kudinsu kai-tsaye daga kason FAAC.
Asali: Legit.ng