Kasafin Kudin 2023: 1.35 Tiriliyan Za a Ware Don Yaki da Boko Haram da ‘Yan Bindiga

Kasafin Kudin 2023: 1.35 Tiriliyan Za a Ware Don Yaki da Boko Haram da ‘Yan Bindiga

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a ware N1.35trn domin yakar Boko Haram da sauran nau’in ta’addanci a 2023
  • Kamar yadda kasafin kudin 2023 da ya mika a gaban Majalisar Tarayya ta nuna, sojin sama, kasa da na ruwa sun fi kowa mora daga kasafin tsaro
  • A cikin kasafin, zasu siya makamai, jiragen yaki da kuma wasu zunzurutun kudi da aka ware domin biyan albashin ma’aikatansu

FCT, Abuja - A yayin da ake cigaba da yaki da matsalar tsaro, gwamnatin tarayya ta ware N1.35 tiriliyan domin cigaba da yaki da rashin tsaron da ya addabi kasar nan.

Wannan na kunshe ne a kasafin kudi N20.51 tiriliyan na 2023 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar tarayyar kasar nan a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

Buhari Budget
Kasafin Kudin 2023: 1.35 Tiriliyan Za a Ware Don Yaki da Boko Haram da ‘Yan Bindiga. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Binciken da Punch tayi ya nuna cewa, daga cikin N1.35 tiriliyan din da ake son warewa, ma’aikatar tsaro da sojoji za a ware musu N1.28 tiriliyan domin yakar Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran rashin tsaro a 2023.

Wadanne hukumomin tsaro ne suka fi samun kasafi?

Daga cikin hukumomin soji 18 na sauran na tsaro, sojin sama zasu samu N174.4 biliyan, sojin masa zasu samu N638.1 biliyan da N158.7 biliyan na sojin ruwa. Wadannan bangarorin ne suka samu mafi girman kaso a kasafin kudin sojin Najeriya.

Ya Za a kashe kudin?

Daga cikin N638.1 biliyan na sojin kasa, N681 biliyan na biyan albashin ma’aikata ne. An ware N108.3 biliyan na kasafin sojin sama domin biyan albashi sai N113.7 biliyan daga cikin na sojin ruwa aka ware domin biyan albashi.

Hedkwatar tsaro tana da kasafin N84.7 biliyan wanda N80.08 biliyan na biyan albashi ne.

Kara karanta wannan

Taliyar karshe: An gano biliyoyin da Buhari da Osinbajo za su ci da sunan kudin abinci da hawa jirgi

Hedkwatar ma’aikatar tsaro an ware mata N32.7 biliyan wanda za a yi amfani da N15.05 biliyan na ma’aikata.

Fitattu daga cikin manyan ayyukan dake kasafin kudin sojin kasan Najeriya akwai siyan makamai, jiragen sintiri da sauransu.

A bangaren na sojin sama kuwa wakai siyan makamai da suka hada da jirage masu saukar ungulu, kudaden kula da wasu jiragen da sauransu.

NAF tana shirin garambawul ga injinan jiragen 6 na Alpha.

Sojin ruwa kuwa zasu siya jiragen ruwa na sintiri, jiragen ruwa na musamman da kuma kafa tashar tsaftace mai har uku.

Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa

A wani labari na daban, an tsananta tsaro a majalisar tarayyan Najeriya kafin zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da kasafin kudin 2023 a yau Juma’a.

Shugaban Kasan zai gabatar da kasafin N19.76 tiriliyan ga zauren gamayya na majalisar dattawa da wakilai da karfe 10 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel