Ku Bari Allah Ya Zaba Muku Shugaban Kasa a 2023, Shawarin Malamin Coci Ga ’Yan Najeriya
- Wani fitaccen fasto a Arewacin Najeriya ya bukaci ‘yan kasar nan, musamman kiristoci su mika wuya ga zabin Allah
- Ya bayyana hakan ne a martaninsa ga zaben 2023 da ake fuskanta nan da watanni kadan masu zuwa
- A cewarsa, Allah ne zai zaba wa Najeriya shugabanni na gari ba mutane ba, don haka kowa ya kula
FCT, Abuja – Gabanin babban zaben 2023 na shugaban kasa, malamai a Najeriya na ci gaba da kira ga ‘yan kasar da su yi watsi da batun addini ko kabilanci, su mai da zabi ga Allah wajen samun shugaba na gaba.
A wannan karon daga Arewa maso gabas, shugaban cocin Seventh Day Adventist, fasto Joshua Mallum ya shawarci ‘yan kasar da su rungumi hadin kai da zaman lafiya tare da addu’ar Allah ya zabawa kasar nan shugaba na gari.
Mallum ya bayyana wannan kiran ne a karshen mako a yayin wani taron cocinsa da aka gudanar a Abuja, jaridar Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa, ya wajaba ga dukkan kiristoci su hada kai, inda yace rabuwar kai ba za ta haifar da komai ba sai tashin hankali da bata zamantakewar juna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mu yi addu'ar Allah ya bamu shugabanni nagari, inji fasto
A kalamansa:
“Ina kira ga dukkan kiristoci da su hada kai. Su yi addu’a, musamman game da zaben 2023 mai zuwa badi. Muna bukatar yin addu’ar Allah ya zaba mana shugabannin da za su sauya abubuwa a kasar.
“Wannan shine kira na ga kiristoci, mu yi addu’a, Allah ne kadai zai iya zaba mana shugananni. Bai kamata mu zaba ma kanmu shugaba ba, kawai mu bari Allah ya zaba mana shugaba na gaba badi.”
Mallum ya kuma bayyana cewa, dalilin da yasa ya kirkiri wannan taro da aka gudanar a Abuja ba komai bane face sake fahimtar da kiristoci manufar zamansu a duniya.
A nasa bangaren, shugaban yankin Arewa ta Tsakiya na cocin SDA, fasto Mikah Nasamu ya ce akwai bukatar kara habaka wa’azin addinin kirista domin isar da sakon ubangiji ga kaso sama da 95% da basu karbi addinin ba.
Fasto Joshua Mallum ya sha bayyana kokensa ga halin da kasar nan ke cewa, a baya Daily Sun ta ruwaito yadda ya yi Allah wadai da kashe-kashen da 'yan ta'adda ke yi a kasar nan.
Ku zabi mijina, inji matar Atiku
A wani labarin kuma, uwar gidan tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Titi Abubakar ta bayyana bukatar a zabi mijinta saboda wasu dalilai.
Ta bayyana hakan ne ga mata Yarbawa na yankin Kudu maso Yamma, inda tace itace za ta zama 'First Lady' ta farko daga yankin.
A cewarta, mijinta zai yaki Boko Haram tare da wanzar da zaman lafiya a yankuna daban-daban na kasar nan.
Asali: Legit.ng