Jerin Wayoyin Da Ba A Amince A Yi Amfani Da Su A Najeriya Ba, NCC Ta Gargadi A Dena Amfani Da Su

Jerin Wayoyin Da Ba A Amince A Yi Amfani Da Su A Najeriya Ba, NCC Ta Gargadi A Dena Amfani Da Su

  • Hukumar Sadarwar ta Najeriya, NCC, ta fitar da jerin wayoyin da ta amince yan Najeriya su biya ba ko amfani da su
  • Hukumar ta kuma yi gargadin yin amfani da wadannan wayoyin yayin da ta yi gargadi game da jabu
  • Mafi yawancin wayoyin da ke jerin ana iya siyansu a kasuwanni a kudi kalilan kamar N2,000

Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya, NCC, ta gargadi al'umma kan siyan wasu wayoyi da amfani da su don ba a amince da su ba.

Hukumar ta kuma sanar da babban hukunci da za ta yi kan yan kasuwa masu sayar da jabun wayoyi ga mutane.

Shugaban NCC
Jerin Wayoyin Da Ba A Amince A Yi Amfani Da Su A Najeriya Ba, NCC Ta Gargadi A Dena Amfani Da Su. Hoto: NCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NCC ta fitar da wannan sanarwar ne bayan tawagarta ta kama wani Yahaya Ado na Gezawa Communications Limited kan sayar da jabun wayoyin kamfanin Gionee.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

Ado, ya kuma gaza nuna izini da ya samu daga hukumar na fara sana'ar wayoyi.

Hatsarin da ke tattare da amfani da wayoyin da ba a amince da su ba

NCC, cikin sanarwar da ta fitar ta yi gargadin cewa amfani da wayoyi da ba a amince da su ba ka iya janyo wa masu amfani da su asara da rashin jin dadin amfani.

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban sashin aiwatarwa na NCC, Mallam Salisu Abdu, wanda ya jagoranci tawgaar, ya nuna damuwarsa kan yadda wayoyin jabu suka cika kasuwar wayoyi da ke Beirut Street, Kano da wayoyin da ba a amince da su ba.

Ga jerin wayoyin da aka haramta amfani da su a Najeriya

  • Wayoyin Gionee masu samfurin G800, da L990
  • Wayoyin H-Mobile masu samfurin it5606+, da H351
  • Wayoyin FoxKong masu samfurin F30, da F300
  • Wayoyin KGTEL masu samfurin K2160 da KG1100.

Jerin wayoyin da aka amince da su

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Delta, inda da dama suka jikkata

Kazalika, shafin NCC ya lissafa jerin wayoyi 1,891 daga kamfanoni daban-daban da aka amince yan Najeriya su yi amfani da su.

Wayoyin da aka lissafo sun hada da na kamfanonin Nokia, Apple, Fero, Motorola, Huawei, LG, Samsung, Sony Ericsson, Itel da sauransu.

Domin duba cikakken jerin, latsa nan.

Hukumar NCC ta gano manhajar 'yan damfara da ake amfani da shi don satar bayanan sirri da dukiyar jama'a

A bangare guda, Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta ce ta gano wata mugunyar manhaja da ake amfani da ita don kutse don sace bayannan sirri na al'umma a wayoyin salula.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, sashen Computer Security Incident Report na hukumar ta NCC ne ya sanar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164