Ba Kamar Atiku Ba, Tinubu Na da Abubuwan Cece-Kuce da Suka Dabaibaye Shi, Inji Dino Melaye
- Kakakin kamfen jam’iyyar PDP ya bayyana kadan daga abubuwan da Atiku ya fi dan takarar APC Tinubu dasu
- Ya ce Tinubu Bola ba mutum ne da komai nasa yake dauke da bayanan gaskiya ba kamar Atiku Abubakar
- Ya kuma siffanta Atiku da dan takarar da zai iya sauya Najeriya zuwa kasa mai ci gaba idan aka bashi dama a 2023
Kakakin gangamin kamfen din jam’iyyar PDP na shugaban kasa, Sanata Dino Melaye ya ikrarin cewa, komai da ke tattare da dan takarar shugaban kasa na APC a cike yake kitimurmura sabanin dan takararsu na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Melaye ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today da gidan talabijin na Channels ya gabatar a jiya Alhamis 1 ga watan Disamba, inda yace Atiku na da nagartaccen tarihi ba kamar Tinubu ba.
Ana ci gaba da luguden lebe tsakanin jiga-jigan siyasan kasar nan tun bayan da aka fara gangamin kamfen, inda kowa ke bayyana alherin nasa tare da kushe kura-kuren abokan hamayya.
A nasa bangaren kuma a wannan makon, Melaye ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Atiku Abubakar mutum ne da za ka karanta tarihinsa da wani ya rubuta, da za ka karanta tarihinsa da ya rubuta da kansa, da za ka karanta tarihinsa da ke rubuce kuma idan ka karanta shekaru 40 ko 30 da suka shude har ila yau shi din dai za ka tarar babu sauyi.
“Za ka iya gano ‘yan ajinsu, za ka iya karanta makarantun da ya halarta, babu wani cece-kuce na daga inda ya fito, Jada, babu wani cece-kuce game da Atiku amma komai game Bola Ahmed Tinubu abin cece-kuce ne, cece-kuce mai ban mamaki.”
Suna bata sunan Atiku da sunan siyasa, martanin Melaye ga batun Oshiomole
Ya kuma yi watsi da jita-jitar da tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole ya yada na cewa, Atiku yace kada ‘yan Arewa su zabi Bayarbe ko Inyamuri daga Kudu a matsayin shugaban kasa, inda yace zancen Adams babatu ne kawai na siyasa.
Melaye ya kuma yi amanna da cewa, Atiku cikakken mai kishin Najeriya kuma shi ne dan takara mafi aminci da nagarta a dukkan wadanda ke son gaje Buhari a 2023, kamar yadda ya shaidawa Channesl Tv.
Ya kuma bayyana cewa, a kokarin neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP, Atiku ya zagaya kasar gaba daya don neman goyon baya kuma aka yi maraba dashi; amma Tinubu ya gaza shiga jihar Kudu maso Gabas na kasar ko da kuwa daya ce.
Melaye ya siffanta Atiku a matsayin biloniya mai kamfanoni halastattu yayin da yace Tinubu biloniya ba tare da kamfani ba.
Daga karshe ya shaida cewa, uban gidan nasa ne dan takarar da zai iya ciyar da Najeriya gaba ta fuskar tattalin arzikin idan ya hada kai da kasuwanni masu kansu.
Matar Atiku ma ta bayyana nagartar mijinta, ta ce shi ya kamata 'yan yankin Yarbawa su zaba saboda ba su damammaki masu yawa.
Asali: Legit.ng