Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ta Yi Masa Girki Da Lalataccen Tumatir, Hirarsu Ta Yadu

Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ta Yi Masa Girki Da Lalataccen Tumatir, Hirarsu Ta Yadu

  • Wani matashi dan Najeriya ya kawo karshen soyayyarsu da budurwarsa bayan ta yi masa miya da rubabbun tumatir
  • A hotunan hirarsu da ya wallafa a Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta kasa cin abincin saboda lalatattun tumatirin da aka miya da shi
  • Da jin haka, sai saurayin nata ya ji babu dadi saboda ciyar da shi abincin da tayi duk da cewar ta san bai kamata a ci ba

Wata hira tsakanin budurwa yar Najeriya da saurayinta da suka rabu kan rubabbun tumatir ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Matashin ya tura budurwarsa kasuwa don siyo kayan abinci. Da ta dawo sai suka lura cewa akwai rubabbun tumatir cikin kayan miyan da suka siyo.

Matashi da sakonni
Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ta Yi Masa Girki Da Lalataccen Tumatir, Hirarsu Ta Yadu Hoto: Danvina_rh
Asali: Twitter

Sai dai kuma, ta yi abinci da shi a haka sannan saurayin nata bai damu ba, yana mai tunanin cewa abun ba zai fito ba tunda za a soya tumatirin.

Kara karanta wannan

Diri suke bi: Mai siyar da abinci ta bayyana yadda maza ke taruwa wajen kasuwancinta don kawai su ga surarta

Lokacin da abincin ya nuna, budurwar ta ki ci sannan ta dage cewa sai dai saurayin ya cinye komai shi kadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya fusata saurayin sannan ya canja mata nan take.

Saurayin wanda ya karaya ya bayyana a hirar tasu:

"Na baki kudina sannan kika je kika siya kayan miya. Kin dawo kika yanka tumatirin sannan kika hada da marasa kyau. Mun lura da haka amma ni na zata ba wani abu bane tunda za a soya shi.
"Amna sai kika soya shi sanna kika yi miyan. Sai kika zuba mun abincin nu kadai. Na tambayi naki, kika ce ba kya jin yunwa. Na lallasheki kan ki ci koda cokali daga ne tunda baki ci komai ba tun safe.
"A nan ne kika samu karfin gwiwar fada mani cewa ba za ki ci ba saoda bai da kyau cin rubabben tumatir. Kin san bai da kyau a ci? Me yasa kika girka mun?"

Kara karanta wannan

Kanwar Maza: Bidiyon Tarairayar da ‘Yan Uwan Amarya Maza 7 Suka yi Mata Wurin Aurenta ya Kayatar

Jama'a sun yi martani

Live with Judith ta ce:

"Ban taba gani ba a rayuwata dalili mara kab gado zai iya zama hujja! Ba zan karyata ba ma, wannan alama ce sosai. Haaaaaaa. Ta yaya zaki ba muthmin da kike soyayya da shi tsawon shekaru uku wanda nake tunanin kina so abincin da ke kanki ba za ki iya ci ba, da haka maita ke farawa da."

Daniel Geezuz ya rubuta:

"Ba zancen miyan bane, batun son kaine kuma lamarin zai sa shi tunani mai zurfi. Mace irin wannan za ta iya sadaukar da kai saboda bukatar kanta."

Wata amarya ta ga gata daga wajen yan uwanta maza 7 a ran bikinta

A wani labarin, wasu samari bakwai sun nunawa kanwarsu gata da tarairaya a wajen shagalin bikin aurenta.

Amaryar ita ce auta kuma mace daya tilo a cikin yan uwan nata lamarin da yasa ta zama ta musamman a wajensu.

Kara karanta wannan

Daga Daina Siyan Datar N9k, Wani Matashi Ya Tara Miliyan A Asusunsa Na Katako

Asali: Legit.ng

Online view pixel