"Dole Ne?" Budurwa Ta Saka Tufafin Amare Ta Tafi Wurin Aikin Saurayinta Tare Da Fasto, Ta Bukaci A Ɗaura Aure

"Dole Ne?" Budurwa Ta Saka Tufafin Amare Ta Tafi Wurin Aikin Saurayinta Tare Da Fasto, Ta Bukaci A Ɗaura Aure

  • Wata kyakyawan budurwa ta gaji da rashin aure don haka ta yanke shawarar daukan mataki kan lamarin
  • Matar, wacce ta gaza hakuri ta ziyarci masoyinta a wurin aikinsa tare da fasto da kawayen amarya ta bukaci a daura musu aure
  • Bayan caba ado da tufafi irin na amare, ta bukaci masoyinta ya yarda a daura musu aure nan take ko kuma ya manta da soyayyar

An yi babban dirama a Target Outlet a Las Vegas bayan wata mata ta shiga wurin ta bukaci masoyinta ya yarda a daura musu aure nan take.

Matar tana sanye da tufafi na amare ta wuce kai tsaye wurin masoyinta ta bukaci ya aure ta nan take.

Budurwa ta tafi wurin saurayi ta ce ya aure ta
"Dole Ne?" Budurwa Ta Saka Tufafin Amare Ta Tafi Wurin Aikin Saurayinta Tare Da Fasto, Ta Bukaci A Ɗaura Aure. Hoto: @bcrworldwide.
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da miji ya kai karar matarsa saboda ya sake ta amma ta ki barin gidansa

Ta zo kantin tare da kawar amarya da wani mutum matashi wanda ta ce fasto ne.

Tana rike da filawa a lokacin da ta shiga kantin ta bawa masoyinta mamaki da neman ya aure ta.

Bugu da kari, ta yi barazanar za ta rabu da shi idan har bai amince ya aure ta ba.

Da ya ke martani kan lamarin, masoyinta ya roke ta su fita waje domin su warware matsalar yadda ya kamata.

Mutane sun yi martani kan bidiyon da ya bazu

Bcr ya ce:

"Wane fasto ya yarda da hakan."

Angelkarri1458 ta ce:

"Haha. Soyayya ta shekara 15 ta ce ka aure ni yanzu. Saurayinta baya son ya rasa aikinsa."

Ci.ndy8802 ya rubuta:

"Soyayyar ta dade da yawa! Ranar karshe ya zo. Yadda saurayinta ya yi martani ne ya birge ni."

Iyanuoluwaadebola ya yi martani:

"Shin wannan wasa ne?"

Pinky.parker.102 ya ce:

"Babban kawar mai rike da filawa ne ta fi birge ni."

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

2384.emmanuel ya rubuta:

"Fasto, wane zabi na ke da shi."

Josephsuberu cewa ya yi:

"Menene haka? Dole ne? Amma dai ba mu san abin da ya faru kafin hakan ba."

Sylvanajohn ta ce:

"Wannan ta gama zarewa."

Aminatou8028 ta ce:

"Tana tilasta masa ya aure ta bata da hankali."

Ga bidiyon a kasa:

Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a

A wani rahoton, wata kotun shari'a a Kaduna, a ranar Litinin ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad ta mayar da katifa ga mijinta da suka kwance alaka, Suleiman Atiku.

Mr Atiku, ma'aikacin hukumar gyaran hali, tunda farko ya bukaci a dawo masa da katifansa, kafin ya amince da bukatar sakinta, The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel