Daga Yanzu Za a Ke Amfani da Harshen Uwa Wajen Koyarwa a Makarantun Firamare, Inji Gwamnatin Buhari

Daga Yanzu Za a Ke Amfani da Harshen Uwa Wajen Koyarwa a Makarantun Firamare, Inji Gwamnatin Buhari

  • A kokarin tabbatar da ilimi ya wanzu a Najeriya, gwamnatin Buhari ta amince a karantar da daliban firamare da harsunan uwa
  • A Najeriya akwai harsuna sama da 625, gwamnati ta ce da su za a ke koyar da daliban firamare a fadin kasar nan
  • Gwamnati ta kuma bayyana cewa, akwai bukatar lokaci don tabbatar da wannan manufa, don haka za ta kula da komai yadda ya dace

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, daga yanzu za a fara amfani da harshen uwa wajen karantar daliban makarantun firamare a kasar nan, TheCable ta ruwaito.

Ministan ilimi na kasar, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zaman majalisr zartaswa ta kasa da shugaba Buhari ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Dalilin Watsi da Dokar Haramtawa K/Napep Amfani da Manyan Tituna Bayan Kwana 1

Adamu ya bayyana cewa, tabbatar da hakan zai ba da wahala, tare da cewa, za a ke gwama harshen uwa da Turancin Ingilishi daga matakin karamar sakandare.

Za a fara karantar da dalibai da Hausa a kasar nan
Daga Yanzu Za a Ke Amfani da Harshen Uwa Wajen Koyarwa a Makarantun Firamare, Inji Gwamnatin Buhari | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

An sanya batun ya zama doka a Najeriya

Harshen uwa dai shine harshe na farko da yaro ke koya bayan da aka haife shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Majalisar zartaswa ta amince da takardar dokar kasa kan lamarin. Don haka, Najeriya a yanzu na da dokar kasa kan harshen gida kuma daga baya ma'aikatar za ta ba da bahasi.
"Daya daga cikin batutuwan dai shine, gwamnati ta amince daga yanzu, ake koyarwa a makarantun firamare - shekaru shida na farin ilimi - da harshen uwa."

A bangare guda, ministan ya ce dokar ta fara aiki daga ranar da aka sanar, amma ana bukatar lokaci don tabbatar da gudanar da ita a makarantu, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: FG Ta Wajabta Fara Koyar Da Daliban Firamare Da Harsunan Hausa, Yarbanci Da Igbo A Makarantun Najeriya

Hakazalika, Adamu ya yi ishara da cewa, Najeriya na da harsuna sama da 625, don haka da su za a ke karantarwa a matakin farko na ilimi, don haka ya zama dole yanzu ake karantarwa da harsunan uwa a kasar nan.

Yayin da ake shirin gyara fannin firamare, har yanzu ana kai ruwa rana da kungiyar malaman jami'a kan batun albashi da kudaden da suke bin gwamnati.

Ya zuwa yanzu, ASUU na ci gaba da barazanar komawa yajin aikin gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu nan kusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.