Babu Wanda Ya Fi Karfin Doka, Alkali Ta Daure Shugaban Sojojin Kasa a Kurkuku

Babu Wanda Ya Fi Karfin Doka, Alkali Ta Daure Shugaban Sojojin Kasa a Kurkuku

  • Kotu ta samu Janar Faruk Yahaya da laifin raina mata hankali, don haka an yanke masa hukuncin dauri
  • Alkali Halima Abdulmalik tace a tsare Shugaban hafsun sojojin kasan a gidan gyaran hali a Minna
  • A hukuncin da aka zartar a jihar Neja, an samu Manjo Janar Olugbenga Olabanji da laifin raina kotu

Niger - Babban kotu da ke zama a garin Minna a jihar Neja, ta bada umarnin a kama shugaban hafsun sojoji na kasa, Janar Faruk Yahaya.

A rahoton da aka samu daga gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, an samu baban sojan kasan da laifin raina kotu.

Baya ga Janar Faruk Yahaya, Alkalin da ta saurari shari’ar, Halima Abdulmalik ta bukaci a cafke shugaban TRADOC, Olugbenga Olabanji.

An samu Manjo Janar Olugbenga Olabanji da irin laifin da shugaban sojojin kasar ya aikata. Daily Post ta tabbatar da wannan rahoton dazu.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Hukuncin Halima Abdulmalik

Mai shari’a Halima Abdulmalik tayi amfani ne da wata dokar aikin gwamnatin jihar Neja ta shekarar 2018 wajen zartar da wannan hukunci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu tace wadannan mutane biyu da ake tuhuma, sun sabawa umarnin da ta bada a ranar 12 ga watan Oktoba 2022, wanda yin hakan laifi ne.

COAS da CDS
Janar Faruk Yahaya da Janar Lucky Irabor Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Halima Abdulmalik ta bukaci a tsare Janar Yahaya da Manjo Janar Olabanji a gidan gyaran hali da ke garin Minna har su iya wanke kansu.

Kotu ba za ta zauna ba sai makon gobe

Bayan ta zartar da wannan hukunci, Alkalin ta daga shari’a zuwa mako mai zuwa. Sai ranar 8 ga wata za a cigaba da sauraron karar a kotu.

Har zuwa yanzu ba a ji wata sanarwa ta fito daga gidan soja a kan wannan hukunci da aka yi wa Janar Faruk Yahaya da Janar O. Olabanji ba.

Kara karanta wannan

Aminu Adamu: Uwargida Aisha Buhari da Mutum 4 Za Su Bada Shaida a Kotu

Bisa dukkan alamu zai yi wahala shugaban hafsun sojojin kasan ya tafi gidan gyaran hali.

Hukunci masu ban mamaki

A baya an ji labarin yadda Mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya zartar da hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ga IGP Usman Alkali Baba.

A watan Nuwamban da ya wuce, Chizoba Oji ya yankewa shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa hukuncin dauri a gidan yari na Kuje.

Aisha Buhari v Aminu Adamu

Rahoto ya nuna Dogarin da yake kare Aisha Buhari ne ya tuntubi Festus Jossiah a kan yadda za a gano duk inda Aminu Adamu yake da zama.

Jossiah yayi amfani da wayar da Aminu yake hawa Twitter da ita, suka bi shi Jihar Jigawa, daga nan aka kudunduno shi har zuwa garin Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng