Gaskiya ta Fito a Kan Zargin Cusa N1.7tr da Minista Tayi a Kasafin kudin Shekarar 2023

Gaskiya ta Fito a Kan Zargin Cusa N1.7tr da Minista Tayi a Kasafin kudin Shekarar 2023

  • Zainab Ahmed tayi wa ‘yan majalisa bayanin dalilin ganin kare-kare a kasafin kudin wasu ma’aikatu
  • Ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya tace an hada ne da ayyukan da za ayi a kan bashi
  • Ahmed ta fita daga zargin da ake yi mata na cewa ta cusa makudan kudi a kundin kasafin shekarar 2023

Abuja - Ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa an yi karin N1.7tr a kasafin kudin wasu ma’aikatu da hukumomi.

Jaridar Premium Times tace Zainab Ahmed ta bayyana wannan ne a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin kasafi na majalisar wakilan tarayya a Abuja.

Ministar tace ma’aikatarta ta sa ayyuka da za ayi a kan bashi a kasafin kudi domin a tabbatar da gaskiya, tace amma ba cushe aka yi wanda ya saba doka ba.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Majalisa Ta Nemi Ministar Buhari Ta Sauka Daga Mukaminta, Ta Faɗi Dalili

Kwamitin majalisar ya gayyaci Ministar ne bayan wasu hukumomi da ma’aikatu sun nuna cewa an cusa masu ayyuka cikin kasafin kudinsu ba da saninsu ba.

Zainab Ahmed tace yanzu gwamnatin tarayya tana rataya ayyukan bashi a ma’aikatun da za ayi su, tace a baya ba a rika sa ayyukan a kasafin kudi ba.

An rahoto Ministar tana cewa tsarin da aka yi amfani da shi wannan karo shi ne yadda aka saba a Duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa
Shugaban majalisar wakilai Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

Kudin da aka kara a ma’aikatun tarayya

A ma’aikatar jin-kai da bada agajin gaggawa, Ministar tace N206bn da aka kara kudi ne da za a rabawa marasa karfi, wanda bankin Duniya ya bada $435.57m.

Rahoton yace haka abin yake a ma’aikatar tsaro, inda aka ware N2.250bn daga cikin N4.5bn da za ayi amfani da su a wajen harkar tsarin makarantu na SSI.

Kara karanta wannan

Karin Farashin Tikiti da Tsare-tsare da Za a Kawo a Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

Daga bayanin Zainab Ahmed, an fahimci cewa N195.4bn da N24.3bn da aka gani a ma’aikatar wuta na ayyukan lantarkin Zungeru da na kamfanin TCN ne.

Ana neman Ministar jin kai

A karshen zaman da aka yi, shugaban kwamitin, Hon. Muktar Betara ya bukaci Ministar jin-kai da bada agajin gagawa, Sadiya Farouq ta bayyana a gabansu.

Ana haka kuma Daily Trust ta rahoto cewa Sadiya Farouq ta wanke Zainab Ahmed daga zargi.

Fetur zai kai N400

A yayin da ake kokawa a kan wahalar man fetur a yau, an samu labari cewa za a iya samun karin 100% kan kowace lita a gidajen mai saboda tashin farashi.

Wani babba a kungiyar IPMAN ya nuna samun fetur ya gagara a tashohin kasar nan, don haka mutane su shirya shan tsada kafin a shiga sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng