Ki Sauka Daga Kujerar Minista Idan Ba Zaki Iya Ba, Majalisa Ta Shawarci Sadiya Farouq

Ki Sauka Daga Kujerar Minista Idan Ba Zaki Iya Ba, Majalisa Ta Shawarci Sadiya Farouq

  • Majalisar wakilan tarayya ta nuna takaicinta da rashin ganin Ministan jin kai duk da gayyatar da aka aike mata
  • Shugaban kwamitin kasafi, Muktar Betara, ya nemi ministar, Sadiya Farouk, ta Sauka idan bata shirya gudanar da aikinta ba
  • Ana ta kai ruwa rana tsakanin majalisar da Ministocin Kudi da jin kai kan wasu kuɗi da aka cusa a Kasafin kuɗin 2023

Abuja - A ranar Talatan nan, majalisar wakilan tarayya ta buƙaci Ministar jin kai, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta sauka daga muƙaminta idan bata shirya aikin da ya dace ba.

PM News ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan gazawarta a lokuta da dama na bayyana a gaban Kwamitocin majalisar domin kare kasafin kuɗin ma'aikatarta.

Sadiya Umar Farouk.
Ki Sauka Daga Kujerar Minista Idan Ba Zaki Iya Ba, Majalisa Ta Shawarci Sadiya Farouq Hoto: nasimsng
Asali: Facebook

Muktar Betara, shugaban kwamitin kasafi shi ne ya faɗi haka yayin zaman bincike kan kutsa biliyan N206bn a kasafin kuɗin 2023 daga ma'aikatar jin ƙai da walwala.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan wata jihar Arewa ya umarci a zaftare albashin ma'aikatan gwamnati

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa ma'aikatar ta ware wa aikin raba ragar sauro Biliyan N206,242,395,000 kuma Bankin duniya ne ke ɗaukar nauyin shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin, Hon. Betara, wanda ya nuna fushinsa a fili ya kalubalanci cewa meyasa Ministar ta gaza zuwa ta kare sanya kuɗin, inda ya kara da cewa idan bata shirya ba ta aje aiki.

"Duk lokacin da Kwamiti ya gayyaci ministar ba ta zuwa. Idan bata shirya aiki ba ya kamata ta sauka kawai," inji Betara.

Daga ina aka samu matsalar tun farko?

Da take bayanin inda aka samu kuskuren tun farko, Minista kudi, Hajiya Zainab Ahmed, tace an cusa abun ne tun a Ofishin Kasafi. Tace ya kamafa ace Ministan jin ƙai ta ankarar da Ofishin kamar yadda takwarorinta suka yi.

Zainab Ahmed tace ma'aikatar tsaro, ma'aikatar makamashi da sauran ma'aikatun gwamnatin tarayya duk sun tafka kuskure amma suka garzaya aka gyara, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

A wani labarin kuma Ministoci Mata Biyu Na Buhari Sun Kaure da Fada Kan Zargin Karin N424bn Na Kasafin Kudin 2023

Ma'aikatar jin kai da walwala ta tarayya karkashin jagorancin, Hajiya adiya Umar Faruk, ta ce an yi kari kan kasafin kudin ma'aikatar ta ne ba tare da saninta ba.

Sai dai da take kare kanta Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta yi bayanin cewa an samu matsalar ne daga na'ura mai kwakwalwa da ake amfani da ita wajen shigar da kasafen kowane ɓangaren gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel