Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Yan Sanda Suka Tarwatsa Masu Zanga-Zangan Neman Murabus Din CJN Da Barkono Tsohuwa

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Yan Sanda Suka Tarwatsa Masu Zanga-Zangan Neman Murabus Din CJN Da Barkono Tsohuwa

  • Birnin Abuja ta shiga rudani a lokacin da yan sanda dauke da makamai suka dira kan masu zanga-zangar lumana da barkonon tsohuwa
  • An tattaro cewa masu zanga-zangar mambobin kungiyoyin cigaban al'umma ne karkashin 'Coalatuin of Civil Societies of Nigeria (CCSN)'
  • CCSN din sun yi tattaki zuwa ma'aikatar shari'a ne suka zanga-zangan neman murabus din babban alkalin alkalan Najeriya, CJN, Maishari'a Tajudeen Ariwoola

FCT, Abuja - Babban birnin tarayya, Abuja, ya shiga rudani a lokacin da jami'an yan sanda dauke da manyan makamai suka tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa, rahoton Vanguard.

An tattaro cewa masu zanga-zangan sun shiga harabar ma'aikatan shari'ar ne a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, suna neman a tsige alkalin alkalan kasa mai ci yanzu, Mai shari'a Tajudeen Ariwoola.

Olayinka Dada
Hotuna sun bayyana yayin da yan sanda ke jefa barkonon tsohuwa ga masu zanga-zangar neman murabus din CJN. Hoto: CCSN.
Asali: Facebook

Hotunan da Legit.ng ta gani ya nuna masu zanga-zanga da dama karkashin 'Coalatuin of Civil Societies of Nigeria (CCSN)' dauke da takardu da rubutu da ke nuna neman tsige CJN din na yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu zanga-zangar sun yi imanin cewa CJN din na yanzu yana nuna bangaranci a siyasa kuma hakan zai iya kawo cikas ga bangaren shari'a ta Najeriya.

Ariwoola must go
Hotuna sun bayyana yayin da yan sanda ke jefa barkonon tsohuwa ga masu zanga-zangar neman murabus din CJN. Hoto: Oasis Magazine.
Asali: Facebook

CCSN din ta yi ikirarin cewa CJN din na yanzu zai iya kawo cikas yayin shari'ar zabuka da za a kawo gaban kotu kafin zabe ko bayan zabe.

Da ya ke magana da manema labarai kan lamarin, Olayinka Dada, kakakin CCSN, ya ce:

"Ganin dimokuradiyyar da aka yi fama da shi yana fuskantar barazana kamar yadda muke gani a yanzu kuskure ne. Yan Najeriya ba za su zuba ido suna kallo ba.
"Yan kwanaki da suka shude, Yan Najeriya sun wayi gari sun yi karo da tsoma bakin da alkalin alkalan Najeriya, Tajudeen Olukayode Ariwoola, ya yi cikin rigingimun yan siyasa wanda hakan na iya saka yan Najeriya cikin yarda da tsarin zaben da za a yi a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Ana Zanga-zanga a Wata Jahar Arewa Bayan Yan Bindiga Sun Harbe Mahaifiyar DPO da Kaninsa

"Ziyara mara tsarki da Alkalin Alkalan Najeriya ya kai jihar Ribas, da aka yi ikirarin kaddamar da aiki ne tare da furta maganganu marasa kan gada game da sabon abokinsa na siyasa Gwamna Nyesom Wike."

"Maganar da CJN Ariwoola ya yi a Ribas ba ta dace ba" - CCSN

Dada ya ce kungiyar ta yi nazarin jawabi wanda bai dace ba da CJN din ya yi a Fatakwal, kuma sun ganin dimokradiyyar Najeriya na iya rushe wa idan Ariwoola ya cigaba da zama CJN.

Ya ce:

"Wannan babban barazana ne ga yin adalci a shari'ar zabe kafin, yayin da bayan babban zaben 2023. Kamar yadda masu iya magana kan ce, wanda ya biya makidi zai zaba irin wakar da za a yi.
"Daga alamun da Tajudeen Olukayode Ariwoola ke nunawa, yana kara fitowa fili cewa babu dan takara ko jam'iyya da za ta samu adalci a kotun koli karkashinsa. Yan Najeriya ba za su saka idanu suna kallo CJN ya lalata mulki mai kyau da suka dade suna ginawa ba tsawon shekaru."

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Nake So a Rika Tunawa da Ni Bayan Na Bar Mulki a Kasashen Afrika

Wasu daga cikin kungiyoyin cigaban al'umma da suka yi zanga-zangar sun hada da Civil Society Forum of Nigeria, Nigeria Youth Development Forum, Democratic Youth Initiative, Forum for Social Justice, da Movement for the Development of Democracy.

Akwai kuma Safeguard Nigeria Movement, Alliance for People's Welfare, Forward Nigeria Movement, Human Right Crusaders, Defenders of Democracy, Democratic Rights Assembly da Voter's Rights Assembly, da wasu.

An yi zanga-zanga a sakatariyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Dandazon masu zanga-zanga sun taru a sakatariyar jam'iyyar APC, a ranar Talata domin nuna rashin amincewarsu da tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi.

Dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu zai bayyana musulmi a matsayin mataimakinsa, inda ya zano Kabir Masari a matsayin wanda zai masa mataimaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164