Bidiyo: Wasu Matasa 7 Sun Baiwa Kanwarsu Kulawa Ta Musamman a Wajen Bikinta, Sun Yi Shigowar Kasaita

Bidiyo: Wasu Matasa 7 Sun Baiwa Kanwarsu Kulawa Ta Musamman a Wajen Bikinta, Sun Yi Shigowar Kasaita

  • Wani bidiyo da ke nuna yadda wata matashiya yar Najeriya ta samu kulawa ta musamman daga wajen yayyenta maza a ranar aurenta ya ja hankali
  • Matasan su bakwai sun sanya kaya iri daya na shadda ruwan bula dinkin babban riga yayin da suka yi shigowar kasaita tare da kanwarsu daya tilo
  • Cike da nutsuwa, sun raba kansu gida biyu yayin da suka saka amaryar a tsakiya inda biyu suka rike hannayenta daga kowani bangare

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun yi ta santi da ganin wani hadadden bidiyon shigowar kasaita da wata amarya da yayyenta suka yi a wajen shagalin bikin aurenta.

Matashiyar ita kadai ce mace a cikin ahlinta, kuma auren nata ya samu halartan dukkanin yayyanta maza.

Amarya da yan uwanta maza
Bidiyo: Wasu Matasa 7 Sun Baiwa Kanwarsu Kulawa Ta Musamman a Wajen Bikinta, Sun Yi Shigowar Kasaita Hoto: TikTok/@northern_hypelady
Asali: UGC

A wani bidiyo da @northern_hypelady ta wallafa a TikTok, wani hadadden kofa ya bude a hankali don bayyana amarya sanye da farin kaya irin na amare.

Nan take, sai yan uwanta maza sanye da bulun shadda dinkin babban riga suka fito inda suka tsaya a gefenta na hagu da dama yayin da ake mata maraba da shigowa filin taron.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun take mata baya a hankali yayin da biyu daga cikinsu suka rike hanayyenta don saukar da ita daga matattakala. Abun ya burge masu kallo.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Silvia ta ce:

"Bata san cewa tana bata masu lokaci bane kada ki yi sauri sai sun barki a wajen."

carolwi4 ya ce:

"Yan uwana basu da lokacina ni kadai ce mace cikin 6 amma nice babba."

Ameenah Musa Duhu ta ce:

"Nice nan, tsakanin maza 8, idan nayi kuskure a nan dukka zasu yi mani."

Exclusiveta ce:

"Gayen da ya rike kanwar tasu ta gefen dama... a zuciyarsa yanzu wannan sai ta tafiya a hankali..bana son kamara ki yi sauri."

Saurayi ya yiwa iyayen budurwarsa sha tara ta arziki, mahaifiyarta ta cika da farin ciki

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi ya gwangwaje dagin budurwar da yake so inda ya dauko su daga unguwar 'ya'yan mallam Shehu zuwa na yan gayu.

Mahaifiyar yarinyar da ta cika da farin ciki ta taka rawa da tsalle domin godiya ga Allah a kan wannan ni'ima da yayi masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel