Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Dan Siyasa a Bauchi, Sun Nemi N100m
- Miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani ɗan siyasa, Hon. Markus Masoyi a kauyen Boi, karamar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun nemi iyalan mutumin su biya miliyan N100m a matsayin kudin fansa
- Shugaban kungiyar cigaban garin ya yi Allah wadai da lamarin, ya nemi jami'an tsaro su matsa kaimi wajen kubutar da shi
Bauchi - 'Yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Boi dake ƙaramar hukumar Bogoro a jihar Bauchi ranar Talata, sun yi awon gaba da wani da aka fi sani da Musa Markus Masoyi.
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilin Tribune cewa da zuwansu 'yan bindigan kai tsaye suka zarce gidansa lokacin kowa na bacci suka tafi da shi.
A cewarsa, maharan sun tafi da mutumin tare da yayansa, wanda daga bisani suka jefar da shi a Jeji, mutane suka tsinto shi suka dawo da shi gida.
Kafin yin garkuwa da shi, Markus Masoyi Sannanen ɗan siyasa ne kuma ya halarci taron gangamin PDP da aka gudanar kwanan nan, har ya ayyana goyon bayansa ga jam'iyyar a 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shin masu garkuwan sun nemi kuɗin fansa?
Bayanai sun ce maharan sun tuntuɓi iyalan mutumin kuma sun nemi miliyan N100m a matsayin kuɗin fansa amma ana ci gaba da tattauna wa har yanzu, mako ɗaya kenan.
Da yake tsokaci kan lamarin shugabn ƙungiyar masu son cigaban Boi, Rabaran Philemon Kicheme, ya bayyana lamarin da abun takaici da kokawa.
"Na ji takaici da karayar zuciya da na samu labarin 'yan bindiga sun yi garkuwa da ɗanmu," inji shi.
Ya ba da tabbacin cewa sun ɗauki matakin da ya dace a kokarin kubutar da ɗan siyasan kana ya yi kira ga hukumomin tsaro su tabbata ya koma cikin iyalansa lami lafiya.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumar 'yan sandan Bauchi ya ci tura sakamakon rashin ɗaukar wayar mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Wakil.
An Bindige Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya
A wani labarin kuma kun ji cewa wasu tsageru sun harbe fitaccen matashin mawaki har lahira a jihar Anambra
Bayanai suka fito sun nuna cewa mawakin kuma marubucin waka, Slami Ifeanyi, ya rasa ransa ne yayin da yake tuƙa sabuwar motar da ya siya a yankin Awka, babban birnin jihar.
Wani aminin abokin marigayin yace duk da basu san dalilin kashe mawakin ba amma wasu alamu sun nuna shiryayyen tuggu ne da nufin ganin bayansa.
Asali: Legit.ng