Tashin Hankali Yayin da Aka Harbe Shugabar Matan Jam’iyyar Labour a Jihar Kaduna
- An samu aukuwar wani mummunan yanayi da ya kai ga mutuwar wata shugabar matan jam'iyyar Labour a wani yankin jihar Kaduna
- An ruwaito cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun kutsa gida shugabar matan tare da yi mata kisan gilla, mijinta ya tsira da munanan raunuka
- A wani labarin kuma, 'yan bindiga dadi sun hallaka shugaban matasan jam'iyyar APC a jihar Ebonyi, an shiga tashin hankali
Kaura, jihar Kaduna - An bindige shugabar matan jam'iyyar Labour ta su Peter Obi, Misis Victoria Chintex a jihar Kaduna yayin da 'yan bindiga suka kutsa cikin gidanta.
An ruwaito cewa, Chintex ce shugabar mata ta jam'iyyar Labour a Kaura ta jihar Kaduna, rahoton PM News.
An kuma bayyana cewa, mijinta ya tsira da raunukan harbin bindiga, an harbe shi a kafa.
Jam'iyyar Labour ta tabbatar da faruwar lamarin
Edward Simon Buju, sakataren yada labarai na jam'iyyar Labour a shiyya ta 3 a jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buju ya bayyanawa Grassroot Reporters cewa, marigayiya Chintex ta kasance mai jajircewa kuma mai sadaukarwa kan ci gaban jam'iyyar su Peter Obi kafin mutuwarta.
Ya kuma bayyana cewa, Najeriya na bukatar irin wannan matar domin tattabar da ci gaba mai dorewa ga 'yan kasar.
Ya kuma yi kira ga mazauna karamar hukumar Kaura a jihar da sauran mabiya jam'iyyar da su kasance masu bin doka da oda, kana ya bukaci 'yan sanda da su tabbatar an bincike kisan Chintex.
Rahoton Pulse.ng ya ce ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaron jihar Kaduna basu tabbatar da faruwar lamarin ba tukuna.
An hallaka shugaban matasan APC a jihar Ebonyi tare da sace wasu mutane 5
A wani labarin kuma kunji cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun hallaka shugaban matasan jam'iyyar APC Hon Celestine Egbuaba a jihar Ebonyi.
Majiya ta bayyana cewa, akalla 'yan bindiga 10 ne suka kai hari yankinsu jigon na APC, inda suka hallaka shi tare da sace wasu mutane daban, inji rahotanni.
A bangare guda, bayan aikata ba, sun yi awon gaba da mutanen biyar zuwa cikin wani daji da ke yankin, kamarin da ya jawo tashin hankali.
Asali: Legit.ng