Gwamnatin Najeriya Tayi Bayani a Kan Wahalar Abincin Da Ake Cewa Za Ayi a 2023

Gwamnatin Najeriya Tayi Bayani a Kan Wahalar Abincin Da Ake Cewa Za Ayi a 2023

  • Gwamnatin tarayya ba ta ganin cewa ambaliyar ruwa da aka yi zai jawo a rasa abin da mutane za su ci
  • Ministan gona da albarakatun Najeriya akwai isasshen kayan abincin da mutane za su ci, ba za ayi yunwa ba
  • Mohammad Abubakar yana ganin babu mamaki abinci ya kara tsada, amma da wuya a rasa abin kai wa baki

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bada tabbaci ga ‘Yan Najeriya cewa akwai isasshen abincin da al’umma za su ci, don haka ba za ayi fama da yunwa ba.

Daily Trust tace Ministan gona da albarakatun kasa, Dr. Mohammad Abubakar ya bada wannan tabbaci ne a taron gabatar da nasarorin gwamnati mai-ci.

Ministan aikin gonan ya amsa tambaya daga manema labarai, yake cewa duk da ambaliyar ruwa da aka yi, ba za a fuskanci matsalar karancin abinci ba.

Kara karanta wannan

Yadda Na Zama ‘Dan Takaran Majalisa Alhali Ina Hannun ‘Yan Bindiga – Sadiq Ango

“Shakka babu, muna da isasshen abincin da za mu ci a kasar nan, amma babu karancin abinci.

Iyakar ta farashi ya karu

Lallai akwai yiwuwar farashi ya tashi, amma zai fi kyau a samu tashin farashi a kan a rasa abincin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna iya ciyar da kanmu da shinkafa, mun fi kowa noman shinkafa a Afrika, mu ne na hudu a Duniya.
Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari a taro: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Mun fi kowa noman rogo da doya, mu ne na biyu bayan Amurka a noman dawa, mu ne na uku a noma gero.
Muna da isasshen abincin da za mu ci, kuma za mu cigaba da kasancewa muna da isasshen kayan abinci.

- Dr. Mohammad Abubakar

Punch tace Ministan ya yi bayani a kan cigaba da Najeriya ta samu ta fuskar noman shinkafa da kuma kamfanonin da aka kafa domin hada takin zamani.

Kara karanta wannan

Karin Farashin Tikiti da Tsare-tsare da Za a Kawo a Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

An yi taron a birnin Abuja wanda shi ne karo na biyar da Ministan yada labarai ya shirya domin tattaro nasarorin Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa yau.

Likitoci na barin Najeriya

An samu rahoto Dr. Emeka Innocent Orji yace an shafe sama da shekaru 10 rabon da gwamnatin tarayya ta karawa Likitoci albash, don haka suke barin kasar.

A duk wata a Duniya, alkaluma sun nuna kasashen waje suna karbe Likitoci 160 daga kasar nan, kimanin Likita 6 a duk rana suke ajiye aiki a Najeriya kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng