Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Kaduna, Sun Samu Nasara
- Sojoji Sun kai farmaki mafakar 'yan fashin daji a yankin karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna
- Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, yace Sojin sun fatattaki yan ta'addan kana suka ceto mutane 9 da aka sace
- Yace sun kuma kwato Mashina da Shanu, a halin yanzun za'a bincika lafiyar mutanen kafin haɗa su da iyalansu
Kaduna - Dakarun Sojin Operation Forest Sanity sun ceto mutane Tara da aka yi garkuwa da su yayin da suka kai samame mafakar yan bindiga a Kaso, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da nasarar sojojin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Yace a bayanan da suka samu na sakamakon Operation ɗin, Sojojin sun buɗe wa yan fashin dajin wuta a Tantatu bisa haka suka yi takansu, suka nausa cikin jeji.
Sojojin basu tsaya nan ba, sun bincika baki ɗaya sansanin inda suka ci karo da mutane Tara da 'yan ta'addan suka ɓoye, suka dawo da su gida.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamishinan yace a bayanan da aka gano kan mutanen, an ce sun shiga hannun masu garkuwan ne a yankin Dam ɗin Gurara.
Aruwan yace Sojojin sun kuma kwato Shanu 90 da yan fashin dajin suka gudu suka bari a sansanin.
"Zamu miƙa Dabbobin da suka kwato hannun hukumar kula da dabbobi domin gudanar da bincike kan masu Shanun a tsanake."
-Aruwan.
A cewar kwamishinan yayin da Sojojin suka kara matsawa da Sintiri har zuwa yankin Bawa Rikasa Hill, sun sake kwato Babura guda huɗu mallakin 'yan fashin dajin.
Yace za'a gudanar da gwajin lafiya kan mutanen da Sojin suka kwato da kuma wasu tambayoyin kafin daga bisani a haɗa su da iyalansu.
Mutanen da sojin suka kubutar sun haɗa da, Salama Oliver, Husseini Odu, Ɗanjuma Jakanwa, Ezekiel Garba, Obadiah Moses, Taiwo Isaac, Buky Isaac, Ado Adamu da kuma Maigari Shekarrau.
Yan Bindiga Sun Sheke Jami’an Yan Sanda Uku a jihar Enugu
A wani labarin kuma Miyagun 'yan bindiga sun yi ajalin jami'an hukumar 'yan sanda guda uku a jihar Enugu dake kudancin Najeriya
Bayanai sun nuna cewa mutane sun shiga yanayin tashin hankali sakamakon abin da ya faru lokacin 'yan sandan na kan aiki a yankin Agbani.
Wannan mummunan al'amari ya afku ne a ranar Asabar, 19 ga watan Numaba da misalin karfe 8:00 na safe a shingen binciken ababen hawa na yan sanda.
Asali: Legit.ng