Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Sheke Jami’an Yan Sanda Uku a jihar Enugu

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Sheke Jami’an Yan Sanda Uku a jihar Enugu

  • Hankula sun tashi yayin da wasu yan bindiga suka halaka jami’an yan sanda uku da ke bakin aiki a yankin Agbani, jihar Enugu
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun farma shingen binciken yan sandan inda suka fara harbi kan mai uwa da wahabi
  • Wannan mummunan al'amari ya afku ne a ranar Asabar, 19 ga watan Numaba da misalin karfe 8:00 na safe

Enugu - Tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a ranar Asabar, yayin wani farmaki da suka kai shingen bincike na yan sanda a garin Agbani da ke karamar hukumar Nkanu ta jihar Enugu.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yan bindigar sun kai mamaya shingen binciken da misalin karfe 8:00 na safe sannan suka budewa jami’an yan sandan da ke bakin aiki wuta inda suka kashe uku a nan take.

Tashar binciken yan sandan na kusa da hedkwatar rundunar na Agbani.

Yan sanda
Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Sheka Jami’an Yan Sanda Uku a Kudu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Vanguard ta kuma rahoto cewa jami’an yan sandan na aikin binciken ababen hawa ne lokacin da makasan suka hange su sannan nan take suka bude masu wuta wanda ya kai ga mutuwar jami’ai uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka yi yan bindigar suka kaiwa yan sandan hari

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana sunansa da Ifeanyi ya bayyana yadda lamarin ya afku.

Ya ce:

“Jami’an yan sanda sun mayar da hankali wajen karbar kudi daga yan achaba da+ direbobin bas ne lokacin da yan bindigar suka farmake su. Lamarin ya faru ne kamar kyafta ido.
“Da yawanmu mun tsere a lokacin da muka ji karar harbi. Mun dawo kawai sai muka ga gawarwakin yan sanda uku.”

Wani bidiyo da aka dauka bayan faruwar lamarin na ta yawo a shafukan soshiyal midiya.

A cikin bidiyon, an gano gawarwakin jami’ai biyu kwance a kasa a gefen wani babban titin

An jiyo wata murya a kasan bidiyon tana cewa:

“Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe jami’an yan sanda yanzun nan. Daya daga cikinsu ya tsere, amma an kashe uku. Kalli gawarwakinsu a nan.”

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ba don baya amsa kiran waya da sakonnin da ke neman jin ta bakinsa kan harin.

Sojoji sun yi luguden wuta kan yan Boko Haram a Borno

Mun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a kan yan kungiyar ta'addanci a yankin Banki da ke jihar Borno.

Sojojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama yayin da suka tarwatsa mabuyarsu a yankin da ke karamar hukumar Bama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel