‘Yan Sanda Sun Yi Magana Kan ‘Kama’ Wanda Ake Zargi Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

‘Yan Sanda Sun Yi Magana Kan ‘Kama’ Wanda Ake Zargi Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

  • Rundunar ‘yan sanda da ke Jigawa ba ta dauke Aminu Muhammadu kamar yadda wasu ke fada ba
  • Aminu Muhammadu ya yi magana a Twitter wanda ake ganin ya ci mutuncin Hajiya Aisha Buhari
  • Tun daga lokacin aka neme shi aka rasa, Kakakin ‘yan sanda yace matashin bai shigo hannunsu ba

Jigawa - Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Jigawa, tace ba ta da hannu wajen cafke wani dalibi mai suna Aminu Muhammad da ake zargin tayi.

Ana zargin Aminu Muhammad yana hannun dakarun ‘yan sanda bisa zargin da ake yi masa na cin mutuncin uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari.

Da aka tuntubi ‘yan sandan jihar Jigawa, sun tabbatar da cewa Aminu Muhammad bai hannunsu, kuma ba su iya yin wani bayanin inda ya shiga ba.

Kakakin rundunar jihar, DSP Lawan Shiisu ya shaidawa Punch cewa bai da labarin jami’an sanda sun dauke wannan dalibin jami’ar FUD a garin Dutse.

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

Bai hannun mu - 'Yan Sanda

Jami’in yake cewa ba za ta yiwu wani ‘dan sanda ya yi ram da matashin ba tare da shi ya sani a matsayinsa na mai magana da yawun ‘yan sanda ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba mu cafke shi ba. Ba zai yiwu a cafke mutum a yankina ba tare da an sanar da ni ba.”

- DSP Lawan Shiisu

Aisha Buhari
Hajiya Aisha Buhari tana jawabi Hoto:guardian.ng
Asali: UGC

DSS ba tace komai ba har yanzu

An nemi jin ta bakin Peter Afunnaya, ya yi bayanin abin da ya sani a kan Adamu Muhammed a matsayinsa na mai magana da yawun jami’an DSS.

Har lokacin da muke tattara rahoton nan, Peter Afunnaya bai amsa kiran wayan da aka yi masa ba, Ana zargin matashin yana hannun jami’an hukumar.

A wani kaulin, hukumar DSS ta cafke Aminu, ta wuce da shi zuwa birnin Abuja, inda aka rika yi masa dukan tsiya a gaban uwargidar shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Matashin yana aji na biyar a jami’ar tarayya da ke Dutse, kuma mutane suna ta yin tir da yadda aka batar da shi ba tare da an gurfanar da shi a kuliya ba.

Ina Aisha Buhari ta shiga?

A taron yakin neman zaben da jam’iyyar APC tayi a Kudu maso Kudancin Najeriya, an ji labari sai dai Zahra Buhari-Indimi ce ta wakilci Aisha Buhari.

Remi Tinubu da ‘yan tawagar ta sun ziyarci fadar Mai martaba Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V yayin da suka roki al'umma su sake zaben APC a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng