Dangote Ya Sanar da Shirin Daukar Matasa 300,000 Aiki, an Fadi Yadda Za a Cika Fom

Dangote Ya Sanar da Shirin Daukar Matasa 300,000 Aiki, an Fadi Yadda Za a Cika Fom

  • Dangote zai fara shirin daukar 'yan Najeriya 300,000 aiki a karkashin shirinsa na rage zaman kashe wando a kasar
  • Sabon shirin na daukar 'yan Najeriya aiki a kamfanin Dangote zai kasance ne a karkashin kamfanonin sukari da man fetur
  • Aikin da za a ba 'yan Najeriya a karkashin matatar man Dangote a Legas zai hada da wurin zama ga ma'aikata 20,000

Aliko Dangote ya sanar da kirkirar ayyuka 300,000 sabbi ga 'yan Najeriya a shirinsa na sake zuba jari a kamfanin sukarinsa.

Wannan daukar aiki mai yawa an sanar dashi ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A cewar rahoton Punch, an naqalto shugaban kamfanin, Aliko Dangote na cewa, zai fadada fannin samar da sukari da kuma kudade shiga ne ga kamfanin.

Wannan shiri nasa na zuwa ne bayan da ya bayyana sabon kudurin daukar aiki a matatar man fetur dinsa da ke Legas.

Kara karanta wannan

Hukumar Sojojin Kasa Tace Zata Canja Fasalin Kai Hare-Hare A Fadin Nigeria

Dangote zai dauki matasa aiki
Dangote Ya Sanar da Shirin Daukar Matasa 300,000 Aiki, an Fadi Yadda Za a Cika Fom | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Attajirin mafi kowa kudi a Afrika ya ce damammakin aikin za su hada da ayyukan kai tsaye da ku ma fakaice.

Ya kuma bayyana cewa, mafi yawa a daukar aikin zai kasance ne a fannin sarrafa sukarinsa da ke jihar Adamawa.

Yadda Dangote je va da gudunmawa wajen rage zaman banza

Kamfanin simintin Dangote, daya daga cikin kamfanonin da Aliko Dangote ya mallaka na daga cikin kamfanonin da ke samar da ayyukan yi a Afrika.

Yawan sanar da ayyukan kamfaninsa yasa aka nada shi shugaban kwamitin samar da ayyukan yi a gwamnatin Najeriya.

An ba shi wannan matsayin ne saboda samar da ayyuka da ya yi ga 'yan Najeriya da dama.

A cewar ma'aikatar masana'antu da zuba hannun jari, matatar man Dangote za ta samar da ayyuka sama da 250,000 idan aka kammala ta.

Kara karanta wannan

Za A Fara Ɗaure Mazinata Da Masu Zaman Dadiro A Gidan Yari A Indonesiya

Ga mai sha'awar cika fom din aikin, sai ya bi wannan likau din zuwa shafin da zai cika.

Abdulsamad ya kara tarin dukiya a 2022

A wnai labarin kuma, Abdulsamad Rabiu na ci gaba da samun riba, yana kusantar matsayin Dangote nan ba da jimawa ba.

Wannan na zuwa ne cikin watanni 11 kacal na shekarar 2022, inda dukkansu biyu suka fara shekarar da wani adadi na kudi.

A bangare guda, Mike Adenuga, mai kudi na biyu a Najeriya ya zama na uku bayan da dukiyarsa ta yi kasa sosai bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.