Abdulsamad Rabiu Zai Karbi Ragamar Dangote Ta Wanda Ya Fi Kowa Kudi a Afrika, Yana Samun N3.4bn a Kullum

Abdulsamad Rabiu Zai Karbi Ragamar Dangote Ta Wanda Ya Fi Kowa Kudi a Afrika, Yana Samun N3.4bn a Kullum

  • Tseren attajiran Najeriya na ci gaba da bunkasa yayin da attajiri Abdulsamad Rabiu ke kara matsowa ga matsayin Dangote
  • A yanzu haka, Abdulsamad ne attajiri na biyu mafi kudi a Najeriya duk da kuwa a 'yan shekaru ukun nan ya fara bunkasa
  • Dangote ne dan kasuwa kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, amma a yanzu Abdulsamad na samun N3.4bn kullum

Abdulsamad Rabiu a yanzu ya zama na biyu a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a Najeriya, kuma yana kusantar matakin Dangote.

Bayanai daga jadawalin Forbes na attajirai ya nuna cewa, ya zuwa ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba, Abdulsamad na da $7bn, babban karin da ya samu daga $4.4bn da ya mallaka a farkon 2022.

Wannan na nufin cewa, attajirin dan kasuwan dan jihar Kano ya samu karin $2.6bn (N1.15tr) a cikin watanni 11 kacal.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya Za tayi Karin Albashi, An Bayyana Ma’aikatan da Abin Zai Shafa

Abdulsamad zai kwace matsayin Dangote
Abdulsamad Rabiu Zai Karbi Ragamar Dangote Ta Wanda Ya Fi Kowa Kudi a Afrika, Yana Samun N3.4bn a Kullum | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Abdulsamad na kusantar matakin Dangote

Bal ma, idan aka raba abin da Abdulsamad ya samu cikin kwanaki 331 na shekarar 2022, a kullum yana samun kimanin N3.42bn.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Forbes ta nuna Abdulsamad a matsayin na 318 a jerin attajiran duniya, kenan ya tashi daga na 719 da yake a Janairun 2022.

Tashin arzikin Dangote a 2022

A karon farko, Dangote ya samu kishiya a fannin kasuwanci da kuma matsayi a jerin attajirai a Najeriya. Dangote ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika duk da kuwa Abdulsamad ya fara bunkasa ainun.

A cewar Forbes, Dangote ya samu $1.3bn a 2022, inda dukiyarsa ta koma $12.9bn ya zuwa ranar Litinin daga $11.6bn na farkon shekarar nan.

Wannan na nuna cewa, gibin arzikin Dangote da Abdulsamad bai wuce $5.9bn ba idan aka kwatanta da $8.5bn na farkon 2022.

Kara karanta wannan

Korarren Akanta-Janar, Ahmed Idris, Ya Mayar Da Kudi N400m Cikin N84.7bn Da Ake Zargin Ya Sata

Raguwar arzikin Mike Adenuga

A bangarensa, 2022 ba shekarar shagali bace ga Mike Adenuga, wanda ya samu raguwar dukiya zuwa $5.6bn idan aka kwatanta da $6.6bn a Janairun 2022.

Raguwar dukiyarsa ke nuna ficewarsa daga matsayin na biyu a jerin attajiran Najeriya.

A yanzu shine mutum na 427 a jerin attajiran duniya.

Duk da haka, Dangote ya bange mutane da yawa a jerin attajiran duniya a shekarar 2022 duba da irin ribar da ya girba a cikin watanni kadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel