Ka Sace Ta Daga Gareni: Kanin Amarya Ya Fada ma Ango a Wajen Shalin Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali

Ka Sace Ta Daga Gareni: Kanin Amarya Ya Fada ma Ango a Wajen Shalin Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wata kyakkyawar amarya ‘yar Najeriya ta cika da farin ciki bayan kaninta ya yi jawabi mai dadi da tsuma zuciya a wajen shagalin bikin aurenta
  • Yaron cikin shiga ta babbar riga ya taya angon murna amma kuma ya fada masa karara cewa ya dauke masa babbar kawarsa
  • Ya kuma bayyana cewa koda dai yana iya fushi da hakan, amma dai ya san cewa hakan ne mafi alkhairi ga yayar tasa

Sakon wani karamin yaro zuwa ga mijin yayarsa a wajen shagalin bikinsu ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

Da yake jawabi a dakin taron, yaron y ace angon ya dauke masa babbar aminiyarsa sakamakon aure ta da yayi.

Amarya, ango da kanin amarya
Ka Sace Ta Daga Gareni: Kanin Amarya Ya Fada ma Ango a Wajen Shalin Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@northern_hypelady
Asali: UGC

Yaron wanda ya koro jawabinsa cikin harshen Turanci ya bayyana cewa yana iya fusata a kan lamarin amma dai yana ganin hakan shine mafi alkhairi ga yayar tasa.

Kalamansa sun zo kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina tayaka murna cewa ka samu aminiyata wacce ka dauke daga gareni.
“Ina iya fusata a wannan yanayin, amma shine mafi alkhairi a gareta.
“Ina godiya gareku yan uwa da abokan arziki.
“Na ji dadin kasancewa a nan. Sai anjima.”

Sakonsa ya kayatar da yayar tasa inda ta dunga murmusawa daga inda take zaune.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Tolabest ta ce:

‘”Na tayata murna.
“Wannan akwai tsuma zuciya.”

Rukayat Omowumi Yusuf ta ce:

“Ka ji ka dauki dangana dan uwa.”

Princess Hikima ta ce:

"Wow ka dauki dangana dan Allah ❤️mun gode da fahimtarka.”

Kyakkyawar matashiya ta koka bayan aurenta na watanni uku ya mutu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kyakkyawar matashiya yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don nuna bakin cikinta bayan aurenta na watanni uku ya mutu.

Kamar yadda matashiyar ta bayyana ciki ba lasisi bane da ke nuna lallai sai ka auri wanda ya yi maka shi don baya nufin samun kwanciyar hankali a gidan aure.

Sai dai kuma, matashiyar wacce ta bayyana mutuwar auren a matsayin mai ciwo bata bayyana ainahin abun da ya sababa rabuwanta da mijin nata ba amma dai ta yi alkawarin sanar da mabiyanta abun da ke ciki nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel