Ministoci Mata Biyu Na Buhari Sun Kaure da Fada Kan Zargin Karin N424bn Na Kasafin Kudin 2023

Ministoci Mata Biyu Na Buhari Sun Kaure da Fada Kan Zargin Karin N424bn Na Kasafin Kudin 2023

  • Ma'aikatar kudi karkashin jagorancin Zainab Ahmad ta fito don yin bayani game da kari da aka samu a kasafin kudin badi
  • Ma'aikatar jin kai da walwala ta kasa karkashin jagorancin Sadiya Umar Faruk ta ce an yi kari kan kasafin kudin ma'aikatar ta ne ba tare da saninta ba
  • Ma'aikatar kudi ta ce an yi kuskuren karin ne wajen amfani da na'ura mai kwakwalwa don shigar da bayanai

Kai komo tsakanin ministocin Buhari biyu mata kan N424bn da aka saka a cikin kasafin kudin 2023 na ma'aikatar jin kai da walwala karkashin jagorancin Sadiya Umar Faruk na ci gaba da tafasa.

Sai dai, ma'aikatar kudi karkashin jagorancin Zainab Ahmad ta yi karin haske kan gaskiyar abin da ya faru har aka samu kari kan kasafin kudin.

Ministar ta kudi ta fito karara ta bayyana inda aka samu kuskure har karin kudin ya shiga ma'aikatar jin kai da walwala.

Kara karanta wannan

Badakala: Majalisa na zargin wata ma'aikata da sace N208m da aka ce an ba 'yan Najeriya

Rikici tsakanin Sadiya Umar Faruk da Zainab Ahmad
Ministoci Mata Biyu Na Buhari Sun Kaure da Fada Kan Zargin Karin N424bn Na Kasafin Kudin 2023 | Hoto: thegazellenews.com
Asali: UGC

An samu matsala ne wajen shigar da kasafin kudin

A cewar Zainab Ahmad, an yi kuskuren shigar da kudaden ne ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa kamar yadda aka saba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, adadin kudin da aka shigar daidai ne kuma hukumomin da suka dace sun amince da hakan.

A cewar rahoton Vanguard, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga ministar kudi, Yunusa Tanko Abdullahi ya ce yiwuwar gano kuskuren da kuma gyara shi bai samu ba daga hukumonin da suka dace.

Ma'aikatar ta kuma yi martani ga zargin da ake yiwa minista Zainab na karin kudi ga kasafin kudin ma'aikatar jin kai da walwala ta kasa.

Abdullahi ya ce, kawai an kirkiri zargin ne mara tushe, saboda karin da ake tunanin an yi ga kasafin kudin bai da makama.

Kara karanta wannan

Kamfanonin Waje na Iya Karbe Jiragen Fadar Shugaban Kasa a Dalilin Taurin Biyan Bashi

Ya kuma bayyana cewa, an yi kuskuren zabi ne a manhajar na'ura mai kwakwalwa, wanda hakan ya nuna za a sayi kayayyakin da suka shafi tsaro a wata hukumar gwamnati.

Wannan kuskuren yasa adadin da aka ambata ya tafi karkashin ma'aikatar jin kai da walwala.

A tun farko, ministar jin kai da walwala ta rubuta wasika ga ma'aikatar kudi, inda ta bayyana zargin shigar da karin kudade kan abin da ta bayar na kasafin kudin ma'aikatarta, NaijaNews ta tattaro.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce da yawa, wanda ya jawo aka fara binciken bangarori daban-daban na kasafin kudin.

Badalakar kudi a ma'aikatar kwadago

A wani labarin na daban, majalisar dattawa ta zargi badakalar kudi a ma'aikatar kwadago ta Najeriya.

Ana zargin an kashe wasu kudade da suka kai N208m ta hanyar da bata dace ba, kuma ba a ba wadanda aka ce za a bai wa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

Ma'aikatar kwadago ta ce ta koyawa 'yan Najeriya sana'a, kana ta basu kudaden sallama a shiyyoyin kasar nan guda shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel