Majalisar Dattijai Ta Zargi Ma’aikatar Kwadago da Badakalar N208m

Majalisar Dattijai Ta Zargi Ma’aikatar Kwadago da Badakalar N208m

  • Majalisar dattawa ta bayyana zarginta ga cinye wasu adadi na kudade a karkashin ma'aikatar kwadago
  • An yi aikin koyar da sana'ao'i a shiyyoyin kasar nan guda shida, an ce an raba kudi ga dukkan wadanda suka halarci shirin
  • Majalisar dattawa na ci gaba da bincike kan wasu kudaden da suka kai N5tr da aka kashe tsakanin 2017 zuwa 2021

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar dattawa mai kula da asusun kudin kasa ya bankado badakalar kudi N208m a ma'aikatar kwadago, inda aka kashe kudin wajen sallamar mutanen da aka koyawa sana'a a wani shiri.

An ruwaito cewa, ma'aikatar ta shirya wani shirin koyar da sana'a ga shiyyoyin kasar nan guda shida a shekarar 2021, wanda aka ware N35m kan kowacce shiyya banda Kudu maso Gabas da ta samu N32m.

Kara karanta wannan

Rikici: Ministocin Buhari biyu sun kaure kan karin kudi a kasafin kudin 2023

An ciro kudin ne daga asusun rarar kudade na kasafin kudi na Service Wide Vote (SWV) domin gudanar da wannan aiki, rahoton Daily Trust.

Majalisa na zargin an cinye wasu kudade a ma'aikatar kwadago
Majalisar Dattijai Ta Zargi Ma’aikatar Kwadago da Badakalar N208m | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamitin majalisar na kan bincika ma'aikatun gwamnati sama da 200 da suka ci kudin da ya kai N5tr tsakanin 2017 zuwa 2021.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ma'aikatar kwadago ta karbi N2.3tr

A bangaren ma'aikatar kwadago, ta karbi N2.3bn daga asusun na SWV tsakanin shekarun da aka ambata, inji takardar da ofishin akanta-janar na kasa ya ba majalisar.

Ma'aikatan ma'aikatar kwadago karkashin jagorancin sakatariyar dindindin Ms Kachollom S Daju sun gabatar da takardun gudanar da shirin koyar da sana'o'in tare da bayyana adadin kudaden da ma'aikatar ta kashe daga kudin asusun SWV.

Sai dai, kwamitin majalisar dattawa karkashin jagorancin sanata Matthew Urhoghide bayan duba cikin tsanaki ga takardun, ya gano cewa, kadan ne daga wadanda suka halarci shirin suka sanya hannun karbar kudi daga shiyyoyin shida na kasa.

Kara karanta wannan

Kamfanonin Waje na Iya Karbe Jiragen Fadar Shugaban Kasa a Dalilin Taurin Biyan Bashi

Da take martani, Ms Kachollom an bi ka'idojin da suka dace wajen rarraba kudaden ga wadanda aka koyawa sana'ar, Punch ta ruwaito.

Sanata Urhoghide ya ce majalisar za ta yi duk mai yiwuwa don daukar mataki ga abin da ma'aikatar kwadagon ta yi.

Badakala da sace kudi na daya daga cikin dalilin da babban bankin Najeriya ya dauko kudirin sauya fasalin kudi a wannan shekarar.

Tuni gwamnati ta kaddamar da kudaden, kuma yace yanzu haka kudin ya fara yawo kuma za a ci gaba da karbar tsoffin kudi zuwa wani lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel