NGF: Gwamnoni 36 Za Suyi Gayya, Za Su Kai Karar Gwamnatin Buhari a Gaban Kotu
- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta NGF za tayi shari’a da gwamnatin tarayya a kan bashin Paris Club
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace ba za su yarda a cirewa jihohi $418m daga kason Paris Club ba
- Aminu Tambuwal ya nuna Gwamnoni suna adawa da batun saida wasu kadarorin gwamnatin tarayya
Sokoto - Kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta dauki matakin shigar da kara a gaban kotu a game da karbar bashin Paris Club da suka karba.
The Cable tace Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal wanda shi ne shugaban NGF ya shaida cewa za su nemi hakkinsu a wajen Alkali.
Kungiyar gwamnonin ta tsaya tsayin-daka a kan cewa gwamnatin tarayya ba za ta ware kudi daga kason Paris Club, ta biya wasu da sunan kwararru ba.
A game da $418m na biyan bashin Paris Club da ma’aikatar tattalin arziki da DMO tayi wa wasu kwararru, kungiyar za ta dage wajen kai maganar kotu.
Za a tabbatar da ko an taba dukiyar jihohi ba tare da hakki ba da sunan za a biya kwararru.
Gwamnoni su hada kotu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Tambuwal yake cewa gwamnoni 36 sun umarci Lauyoyinsu da su je kotun tarayya domin a dakatar da maganar saida tashoshin wuta na NIPPs.
Jaridar tace gwamnonin ba su goyon bayan shirin da gwamnatin tarayya take yi na saida NIPPs goma, don haka suke so su kawo yunkurin burki ta kotu.
Abin da kungiyar ta NGF take so shi ne kotu ta hana a cigaba da maganar saida dukiya da kamfanin lantarki na NDPHC wanda Neja Delta ya mallaka.
Ambaliyar ruwan sama
Rt. Hon. Tambuwal yace NGF tana so a sa idana a game da abubuwan da suka shafi kasar nan kamar sha’anin ambaliya, rigakafin cutar foliya da sauransu.
Gwamnonin sun hada-kai da majalisar NEC, hukumar NEMA, da ma’aikatun tattalin arziki, bada agajin gaggawa da bankin Duniya wajen magance annoba.
Farfesa Foluso Okunmadewa na bankin Duniya ya yi wa kungiyar gwamnonin bayani kan yadda za a gyara tsarin CARES ta yadda za a tallafawa jama’a.
Karin albashin NBA
An ji labari Ministan kwadago ya yi zama da Shugabannin kungiyoyin Likitoci da wasu ma'aikatan lafiya, sun kawo masa wasu koke-koken da suke da shi.
Yau fiye da shekaru 10 da yin alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta rika karawa likitoci albashi a Najeriya, amma har yau shiru babu labarin yin hakan.
Asali: Legit.ng