Sababbin kudi: EFCC da ICPC Za Su Sa Ido Kan Masu Cire Makudan Kudi Inji CBN
- Gwamnan CBN yace yanzu mutum bai isa ya je banki ya nemi cire makudan kudi daga asusunsa ba
- Godwin Emefiele ya tabbatar da cewa kafin a iya daukar kudi masu yawa, sai an karbi bayanan mutum
- Wannan zai ba hukumomi irinsu ICPC da EFCC damar sanin duk inda aka shigar da wadannan kudi
Abuja - Gwamnan babban bankin kasa na CBN, Godwin Emefiele yace za su yi aiki da jami’an hukumomin EFCC da ICPC wajen zura idanu a bankuna.
Guardian ta rahoto Godwin Emefiele yana mai cewa za su hada-kai da wadannan hukumomi domin a rika bibiyar wadanda ke cire kudi masu yawa.
Mista Emefiele ya yi wannan bayani a sa’ilin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja a wajen bikin kaddamar da sababbin kudin da aka buga.
Gwamnan babban bankin yake cewa adadin kudin da mutum zai iya cirewa daga asusu a cikin banki zai ragu saboda tsare-tsaren da CBN zai kawo.
Kudi zai rage yawo a gari
Wannan yana cikin kokarin CBN na ganin kudin da ke yawo a hannun jama’a ya ragu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan dole sai mutum ya cire kudi masu yawa daga asusun banki, Emefiele yace za a hada shi da tulin takardu da zai cike saboda a dauki bayanansa.
Da zarar mutum ya shiga banki ya karbi masu yawan gaske, za a shiga bin sahunsa domin tabbatar da cewa ba wani aikin assha zai yi da wadannan dukiyar ba.
“Za mu rage adadin kudin da mutane za su iya cirewa a cikin banki. Idan kana neman kudi da yawa, sai ka cika fam barkatai – bila-adadin.
Za mu dauki bayananka, daga BVN zuwa NIN ta yadda jami’an hukumomin EFCC da ICPC za su iya bibiyarka, a ga aikin da za ayi da kudin.
- Godwin Emefiele
Ba wani ake hari ba - CBN
Punch ta rahoto Gwamnan babban bankin yana cewa ba a shigo da wannan tsari saboda ayi kokarin ganin bayan kowa ba, illa iyaka a samar da gyara.
A lokutan baya, Emefiele yace an nemi a buga sababbin kudi, amma wasu suka hana hakan tabbata. Sai a shekarar nan ne dai maganar ta zama gaskiya.
Babu maganar buga jabu
Rahoto ya zo cewa Muhammadu Buhari yace a Najeriya aka buga sababbin kudin, ya kuma yi bayanin fa’idojin da za a samu a dalilin canjin da aka yi.
Dama can a kowane shekaru 5 zuwa 8 ake bukatar a fito da sabon kudi, Muhammadu Buhari yace takardun da aka sauya sun fi shekaru 20 a Najeriya.
Asali: Legit.ng