‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane, Sun Ce da Sababbin Kudi Za a Biya Fansar N5m
- ‘Yan bindiga sun dauke mutane akalla hudu a wani hari da aka kai wa Kauyen Kolo da ke jihar Zamfara
- Wani mazaunin garin yace miyagun sun ce sababbin kudin da aka buga suke bukata a aiko masu a jeji
- A shirye ‘yan ta’addan suke da su cigaba da rike wadannan mutane har zuwa lokacin da kudin za su fito
Zamfara - Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne, sun dauke mutane hudu a jihar Zamfara, daga ciki akwai wani Bawan Allah da mace da kuma yara biyu.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Larabar nan, tace wannan labari mara dadin ji ya auku ne a garin Kolo da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Wadannan ‘yan bindiga sun ki karbar kudin fansar da aka kai masu na miliyoyn Nairori, sun nemi a aiko masa da sababbin kudin da bankin CBN ya buga.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru, Mohammed Ibrahim yace ‘yan bindigan sun rage kudin fansar da suka lafta daga Naira miliyan 10 zuwa Naira miliyan 5.
Ana neman inda kudi za su fito
Mohammed Ibrahim ya fadawa manema labarai cewa mutanen garin na Kolo suna ta kokarin hada kudin da za a biya domin a iya ceto ran wadannan mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Muna kokarin tattara kudin da ‘yan ta’addan suka bukata, sai suka sake aiko mana sakon nan da safe cewa ba za su karbi tsofaffin kudi ba.
Sun ce za su cigaba da rike mutanen da suka tsare a hannunsu zuwa lokacin da za a fitar da sababbin kudin da aka buga a watan Disamba.”
- Mohammed Ibrahim
Jami'an tsaro ba su ce uffan ba
An nemi Kwamishinan ‘yan sandan reshen Zamfara domin jin ta-bakinsa, amma a ba dace ba. Haka zalika kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara.
Rahoton da gidan talabijin na Channels ya fitar dazu ya nuna jami’an tsaro ba su iya cewa komai a game da wannan lamari ba har zuwa yammacin yau.
An sace Nduka Anyanwu
Ana haka ne kuma sai ga shi ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da Nduka Anyanwu a jihar Imo. Anyanu yana cikin jiga-jigan jam’iyyar APGA a Kudu maso gabas.
Ko da shugaban APGA na reshen Imo, John Iwuala, ya tabbatar da abin da ya faru. Kakakin ‘yan sandan jihar, Mike Abattam bai da masaniya kan lamarin.
ASUU ta cigaba da jan daga
Labari ya zo cewa kungiyar ASUU tace a halin yanzu tana rama duk ayyukan da ba tayi ba a samakon yajin-aikin da tayi, don haka dole a biya ta albashinta.
Gwamnatin Tarayya ta dage a kan cewa ba za ta biya ma’aikaci kudin aikin da bai yi ba, hakan ya yi sanadiyyar da Malaman jami’a suka fito da wata dabara.
Asali: Legit.ng