Gwamnatin Najeriya Ta Juyo Kan Manyan Masu Kudi, Tana So a Lafta Masu Haraji

Gwamnatin Najeriya Ta Juyo Kan Manyan Masu Kudi, Tana So a Lafta Masu Haraji

  • Ben Akabueze ya fara maganar tatsar manyan Attajirai saboda gwamnatin Najeriya ta samu kudi
  • Darekta-Janar na ofishin kasafin kudin kasar yana ganin masu kudi ba su biyan harajin da ya kamata
  • Akabueze yace bai kamata a kyale mutane suna samun makudan kudi, amma ba su ba kasarsu komai ba

Abuja - Darekta-Janar na ofishin kasafin kudin tarayya, Ben Akabueze yace akwai bukatar ‘Yan Najeriya masu kudi su rika biyan haraji yadda ya dace.

The Cable ta rahoto Ben Akabueze a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba 2022, yana mai bada shawarar a dage a samu kudin shiga ta hannun masu kudi.

Akabueze ya yi wannan bayani a garin Abuja a wajen bikin kaddamar da wani rahoto na bankin Duniya kan halin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki.

Bankin Duniya ya bada shawarar gyare-gyaren da za ayi domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Wike Ya Tona Kudin da Buhari Ya Rabawa Jihohi, Gwamnonin Kudu Sun Shiga Runtsi

Idan an samu kudi, sai a biya haraji

Darekta-Janar din yana da ra’ayin cewa abin da ya fi dacewa shi ne manyan masu kudi su rika biyan harajin da ya yi daidai da irin dukiyar da suke samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Najeriya
Gabatar da kasafin kudi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Muna bukatar mu sa haraji a kan masu kudi. Muna da gawurtattun masu kudi, suna rayuwa tare da masu fama da rikakken talauci.
Ina ganin wannan a matsayin wata manakisar mala’u na hana dukiyar kasa ta rika yawo.
Idan ka na da jirgin sama na kan-ka, hakan ya yi kyau. Idan ka saye daya, sai ka sayawa kasarka daya ta hanyar biyan haraji 100%.
Akwai bangarorin da ke bunkasa a yanzu da ya kamata su rika biyan haraji. Bangaren fikira da basira da masu yada labarai.
Akwai mutanen da ba su da ayyukan yi illa su rika yi mana kwalele, suyi ta nuna mana sababbin motocinsu.

Kara karanta wannan

EFCC ta sha Alwashin Gwangwaje Duk Wanda ya Fallasa Boyayyin Kudi da 5% na Jimillarsu

Babu wata mafita. Dole ne mu tatsi masu kudi. Su biya harajin da za iyi daidai da dukiyar da ke shigowa aljihunsu."

- Ben Akabueze

Rahoton Nairametrics ya nuna shugabar ofishin DMO, Patience Oniha da Doyin Salam sun yi jawabi na musamman a wajen wannan taro da aka yi.

EFCC tayi nasara a kotu

Labari ya zo dazu cewa Jonah Otunla da Kanal Bello Fadile sun rasa dukiyoyinsu a sakamakon nasarar da Lauyoyin EFCC suka samu a kansu a kotu.

Jonah Otunla ya rike Akanta Janar a Najeriya yayin da shi kuma Bello Fadile ya yi aiki da Kanal Sambo Dauki a NSA a Gwamnatin Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel