Atiku Zai Gyara Kura-Kuran da PDP Ta Yi Daga 1999 Zuwa 2015, Inji Jigon PDP

Atiku Zai Gyara Kura-Kuran da PDP Ta Yi Daga 1999 Zuwa 2015, Inji Jigon PDP

  • Jigon jam’iyyar PDP ya bayyana cewa, Atiku ne zai iya gyara kasar nan, kuma zai tabbatar komai ya tafi yadda ake bukata
  • Doherty ya amince PDP ta tafka kura-kurai a shekarun baya, amma ya ce a yanzu za ta gyara komai bayan Atiku ya lashe zabe
  • A bangare guda, ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su sake ba APC damar sake mulkin kasar nan ba har abada

Jihar Legas - Doherty ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta PDP ta tafka wasu kura-kurai a lokacin mulkinta tsakanin 1999 zuwa 2015, amma Atiku zai gyara komai daga kura-kuran PDP.

Doherty, wanda kuma shi ne shugaban tawagar gangamin Atiku da Okowa a jihar Legas, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a Najeriya jim kadan bayan fara kamfen.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Atiku zai gyara kura-kuran PDP idan ya gaji Buhari, inji jigon PDP
Atiku Zai Gyara Kura-Kuran da PDP Ta Yi Daga 1999 Zuwa 2015, Inji Jigon PDP | hOTO: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, PDP ta sauya wasu abubuwa da dama nata, kuma tabbas ta yi kura-kurai a baya, amma ta yiwa ‘yan Najeriya alkawarin daidaita lamurra bayan zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma shaida cewa, Atiku ya taimaka a baya wajen habaka tallalin arzikin kasar nan bayan da kasar ta koma mulkin dimokradiyya daga mulkin soja a 1999.

Atiku dai ya kasance mataimakin shugaban kasa ga tsohon shugaba Obasanjo daga 1999 zuwa 2007 bayan da suka karbi mulki a hannun Abdulsalami Abubakar.

APC bata cancani sake mulkin Najeriya ba

A bangare guda, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki, inda yace duba da abin da ta yid aga 2015 zuwa yanzu, bai kamata ‘yan Najeriya su kara bata dama ba, kamar yadda ya shaidawa Channels Tv.

Duk da kalaman da ya yi, jam’iyyar PDP bata taba mulkin jihar Legas ba tun daga kan Tinubu a 1999 har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

Najeriya na ci gaba da daukar zafi tun bayan da aka fara gangamin kamfen a kasar nan, kowa na cewa shi ya cancanta ya gaji Buhari.

A wani labarin kuma, wani jigon APC ya bayyana cewa, Najeriya ba kasar addini bace, kuma ba yadda hakan zai zama matsala ga makomai siyasar Tinubu.

Ya ce gamin Musulmi da Musulmi na APC ba komai bane face tsagwaron siyasa mai tsafta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.