Jami’an Tsaro Sun Ci Karfin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Daga Hannun Miyagu
- Sojoji da ‘Yan sanda sun iya ceto wasu fasinjoji da aka yi garkuwa da su tsakanin Kaduna da Katsina
- Jami’an tsaro sun samu labarin ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da fasinjoji 76 da suka fito daga Sokoto
- Jawabin dakarun ya nuna yanzu wadannan Bayin Allah sun kubuta, an iya fatattakar ‘yan bindigan
Kaduna - Dakarun ‘yan sanda da sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane a kan hanyar Funtuwa zuwa garin Zariya da ke jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa jami’an tsaro sun ceto wadannan matafiya ne a yankin Gulbala da ke karamar hukumar Giwa a Kaduna.
Kamar yadda rundunar ‘yan sandan reshen Kaduna suka bayyana, an kubutar da fasinjojin a ranar Juma’a da samun labarin ‘yan bindiga a Giwa.
DSP Mohammed Jalige ya fitar da wani jawabi yana cewa sun samu labarin ‘yan bindiga da yawa sun zo dauke da manyan makamai sun tare titi.
Jami'an tsaro sun shiga bakin aiki
Da jin miyagun ‘yan bindigan suna yunkurin tare fasinjoji a titi, sai jami’an tsaro suka yi azama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed Jalige yace nan-take dakarun ‘yan sanda da sojoji suka ruguza shingen da ‘yan bindigan suka sa, suka kakkabe miyagun ‘yan bindigan.
Kakakin ‘yan sandan yace da isa inda ‘yan bindigan suka tare har suka dauke mutane, sai aka ci karo da mota kirar Ford mai lamba APP 667 XG.
Jawabin yace ‘yan bindigan sun dauke tulin fasinjojin da ke cikin wannan mota. Daga nan sai sojoji da ‘yan sanda suka shiga jeji domin a ceto su.
A karshe ta'adi bai yiwu ba
A karshe dai jami’an tsaron sun yi nasara, ‘yan bindigan suka hakura da yin gaba da fasinjojin.
Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku yace an samu wannan gagarumar nasara ne a sakamakon hadin gwiwar jami'an tsaro da aka samu.
Bincike ya nuna fasinjojin da aka tare suna kan hanyar zuwa Sabon Birni ne a garin Sokoto. Rahoton yace fasinjojin da aka shiga jeji da su sun haura 70.
Zargin satar danyen mai
Rahotanni sun tabbatar da zargin satar dukiyar man Najeriya ya jawo sojoji shiga kotu da wasu ‘Yan Kasar Waje domin a yanke hukuncin da ya dace.
An ga jirgin da ya dauko wasu ‘yan kasashen Indiya, Foland, Fakistan da Sri Lanka a wajen rijiyoyin mai, ana zarginsu da sata, zargin da sun musanya.
Asali: Legit.ng