Kwamandan ‘Yan Bindiga, Dankarami, Ya Sace Mutum 44 Bayan Kutsawa Gida-gida a Kanwa

Kwamandan ‘Yan Bindiga, Dankarami, Ya Sace Mutum 44 Bayan Kutsawa Gida-gida a Kanwa

  • Miyagun ‘yan bindiga karkashin jagorancin kwamanda Dankarami sun sace mutum 44 a yankin Kanwa dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara
  • Mazauna yankin sun ce miyagun sun shiga gida-gida inda suka dinga tasa keyar mata da kananan yara, har yanzu basu nemi kudin fansa ba kuma
  • Hakan na faruwa ne yayin da ake tsaka da hada N20m ta kariya a garin Moriki kamar yadda kungiyar Turji ta bukata don bai wa jama’ar yankin kariya

Zamfara - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da a kalla mutum 44 daga yankin Kanwa dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta tattaro hakan.

‘Yan bindigan Zamfara
Kwamandan ‘Yan Bindiga, Dankarami, Ya Sace Mutum 44 Bayan Kurosawa Gida-gida a Kanwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindiga sun tsinkayi yankin da dare inda suka dinga shiga gida gida tare da sace jama’a wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara.

Kara karanta wannan

Miyagun ‘yan Bindiga Sun Harbe ‘Yan Sanda 3, Sun Sace Hamshakin mai Arziki

A cikin kwanakin nan an samu sauki a wasu yankuna amma yanzu kuma farmakin sun dawo, lamarin da yasa jama’ar yankunan ke zaman tsoro.

Shugaban ‘yan bindiga Dankarami ne yayi satar

An sakankance cewa wannan satar jama’a masu yawan aikin rikakken ‘dan bindiga Dankarami ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto cewa, Dankarami shi ne shugaban ‘yan bindigan da ya addabi yankunan Zurmi, Birnin Magaji, Jibia har da wasu sassan jihar Katsina.

Yace ‘yan bindigan har yanzu basu kira ‘yan uwan wadanda suka sace ba domin neman kudin fansa.

Mazauna Moriki suna hadawa Bello Turji N20m ta kariya

A daya bangaren, mazauna garin Moriki sun fara kokarin bayar da kudin kariya bayan ‘yan bindigan sun bukaci kudi har N20 miliyan daga mazauna yankin.

Kudin harajin da aka kallafa musu ana tattara su ne gida gida kuma za a kai shi sansanin Bello Turji bayan kungiyar tace idan suka biya kudin za a basu kariya daga farmaki.

Kara karanta wannan

Osun: Rikicin Sarauta ya Barke, An Bindige Yarima Lukman Har Cikin Fada

Moriki na nan a wuraren titin Shinkafi da Kauran Namoda kuma suna fuskantar tsananin cin zarafi daga ‘yan bindiga wanda ya hada da sace malaman makarantar ‘yan mata ta gwamnati a baya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu bai samu yin tsokacin kan lamarin ba tunda ba a riga an same shi a waya ba.

Yan Sanda sun cafke dagacin kauye dake hada kai da ’yan bindiga

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun damke dagacin Gobirau a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Ana zarginsa da hada kai da ‘yan bindiga wurin halaka Yahaya Danbai, ba jarumin manomi a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel