‘Yan Bindiga Sun Aika ‘Yan Sanda 3 Barzahu, Sun Sace Wani Babban Mutum

‘Yan Bindiga Sun Aika ‘Yan Sanda 3 Barzahu, Sun Sace Wani Babban Mutum

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kai mummunan farmaki kan ayarin motocin wani babban mutum a Fatakwal inda suka halaka jami’an ‘yan sanda hudu
  • An gano cewa, sun yi tawagar kwantan bauna a gadar sama inda suka ritsa su tare da harbe-harbe har da sace babban mutumin
  • Ba a nan suka tsaya ba, sun kwashe wasu tsabar kudi da suka tarar a motarsa yayin da suka firgita jama’a da harsasansu ta hanyar harbi

Fatakwal, Ribas - ‘Yan bindiga sun kai farmaki kan ayarin motoci kuma sun halaka ‘yan sanda hudu dake bai wa wani babban mutum tsaro a Fatakwal dake jihar Ribas, jaridar Punch ta bayyana.

Miyagun ‘yan bindiga da ‘yan sanda
‘Yan Bindiga Sun Aika ‘Yan Sanda 3 Barzahu, Sun Sace Wani Babban Mutum. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Miyagun sun yi garkuwa babban mutumin tare da yin awon gaba da tsabar kudin da har yanzu ba san yawansu ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Osun: Rikicin Sarauta ya Barke, An Bindige Yarima Lukman Har Cikin Fada

An gano cewa, sun kai musu farmaki wurin karfe 3 na yammacin Alhamis kan sabuwar babbar gadar Rumuokoro dake karamar hukumar Obio/Akpor.

‘Yan bindigan sun yi shiga cikin kayan sojoji kuma sun sha gaban tawagar motocin inda suka halaka ‘yan sandan tare da cigaba da harbi babu kakkautawa kafin su yi garkuwa da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa, miyagun sun yi kwantan bauna a wurin tun farko inda suka dinga jiran tawagar.

Ganau ya bayar da labari

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, wata majiya wacce ta kasance ganau kan abinda ya faru, tace ‘yan bindigan cike da kwarin guiwa suka ci karensu babu babbaka balle hantara, lamarin da ya gigita jama’a a yankin.

Yace:

“Da ranan nan wurin karfe 3 na yamma, muka dinga jin harbi a gadar sama. Da farko zatonmu jami’an tsaro ne suke harbin saboda a kayan sojoji suke.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Hadimin Gwamnan APC

“An cigaba da harbin yayin da motocin dake kasan gadar suka tsaya na dole. ‘Yan bindigan sun halaka ‘yan sanda hudu dake yi wa mutumin rakiya.
“Sun kwashe kudin da suke tare da tawagar tare da yin garkuwa da mutumin. Bayan nan, sun shige motarsu inda suka cika bujensu da iska.”

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Gracew Iringe-Koko, ‘yar sanda mai mika min sufirtandan, ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace ‘yan sanda uku abun ya ritsa dasu.

Yan bindiga sun kai hari caji ofis

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo muku cewa ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda a jihar Ondo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Odunlami Funmilyai ya tabbatar da faruwar lamarin inda ce musayar wuta aka yi a tsakanin miyagun da ‘yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel