‘Yan Sanda Sun Damke Dagaci Kan Hada Kai da ‘Yan Bindiga a Katsina

‘Yan Sanda Sun Damke Dagaci Kan Hada Kai da ‘Yan Bindiga a Katsina

  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da kama dagacin kauyen Gobirau dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • An kama Malam Surajo Madawaki da zargin hada kai da ‘yan bindiga wurin halaka wani zakakurin manomi da ya nuna bajintarsa ta fin karfin ‘yan bindiga
  • An kai masa hari a gona amma yafi karfin miyagun ya kwace bindigarsu tare da kai wa dagacin, sai dagacin ya kira wasu ‘yan bindiga da suka kwace bindigar tare da halaka manomin

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani Surajo Madawaki, dagacin Gobirau dake karamar hukumar Faskari kan zarginsa da hada kai da ‘yan bindiga wurin halaka manomi, jaridar TheCable ta rahoto.

Taswirar Katsina
‘Yan Sanda Sun Damke Dagaci Kan Hada Kai da ‘Yan Bindiga a Katsina. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A yayin jawabi ranar Juma’a yayin bayyana kamen, Gambo Isah, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar yace rundunar ta samu kiran gaggawa kan cewa ‘yan ta’adda sun halaka wani Yahaya Danbai mai shekaru 35 yayin da yake aiki a gonarsa.

Kara karanta wannan

Yaki da Ta’addanci: ‘Yan Sanda Sun Ragargaza ‘Yan Bindiga 7 a Neja

Danbai yafi karfin ‘yan bindiga

Yace ‘yan bindigan sun fi karfin Danbai kuma sun kashe shi inda ya kara da cewa manomin ya kai wa dagacin kauyen rahoto, jaridar P.M News ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Isah yace dagacin kauyen bayan samun bayanin ya ki kiran ‘yan sanda amma sai ya hada baki da wani ‘dan bindigan kan ya kawo masa bindigar da aka samo daga shugaban ‘yan bindigan farko.

“Manomin yayi ta maza inda ya fi karfin masu son halaka shi tare da kwace bindigarsI kirar AK-47 kuma ya kai kara wurin dagacin, Malam Surajo Madawaki mai shekaru 50.”

- Takardar tace.

Dagaci Surajo ya hada baki da ‘yan bindiga

“A maimakon kai wa ‘yan sanda rahoto, dagacin ya kira wani Hamisu, fitaccen shugaban ‘yan bindiga inda ya mika masa bindigar da manomin ya kwato.

Kara karanta wannan

Bayan fitowarsa daga Kurkuku ranar Juma’a, an kamashi ranar Asabar yana sake tafka sata

“Daga bisani, Hamisu ya kira mukarrabansa, sun zagaye kauyen inda ya zakulo zakakurin manomin tare da halaka shi a take.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa, wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne sun sanya harajin miliyan 10 kan kauyen inda suka yi barazanar halaka dukkan mazauna yankin idan suka ki biya.

“Tun bayan nan, dagacin garin ya boye amma daga bisani an kama shi.”

- Ya kara da cewa.

“A yayin bincike, dagacin kauyen ya amsa cewa yana da hannu a cikin aikata laifin.”

‘Yan Sanda sun halaka ‘yan bindiga 7 a Neja

Legit.ng ta rahoto muku yadda jami’an ‘yan sandan jihar Neja suka ragargaji ‘yan bindiga bakwai a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel