Shehu Sani Ya Gargaɗi China: Ku Yi Taka Tsantsan Da Ba Wa Najeriya Bashi

Shehu Sani Ya Gargaɗi China: Ku Yi Taka Tsantsan Da Ba Wa Najeriya Bashi

  • Kwamared Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya gargadi China kan ba wa Najeriya bashi
  • Sani ya yi kira ga mahukunta a kasar na China su rika tabbatarwa kudin da za su bayar za a yi ayyukan da za su kawo cigaban kasa ne
  • Mai rajin kare hakkin bil adaman ya kuma yi kira ga jam'iyyar Communist na China ta rika gayyatar jam'iyyun Najeriya taronta don su koyi yadda ake ciyar da kasa gaba

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya yi kira ga kasar China ta yi taka tsantsan wurin ba wa Najeriya bashi, rahoton Daily Trust.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin da ya ke magana wurin wani taro da Cibiyar Nazarin China (CCS) ta shirya.

Shehu Sani
Shehu Gani Ya Gargaɗi China: Ku Yi Taka Tsantsan Da Ba Wa Najeriya Bashi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ke yaba wa China wurin kawo cigaba a Najeriya da Afirka baki daya, ya ce China ta rika bada bashi ne kawai wanda zai kawo sauyi a rayuwar yan Najeriya.

Ya ce:

"Yana da muhimmanci duk da kasarku na son tallafawa Najeriya wurin aiwatar da ayyukanta, a sani cewa wadanda ke gwamnati suna wurin ne na dan lokaci.
"Bashin da za a karbo a kasarku ya kasance mai muhimmanci, wanda zai kawo canji a tattalin arzikin kasar.
"Za ku iya taimaka mana da bashi kuma kuna iya yin hakan ta hanyar wadanda suka zo wurin ku. Ku samu karfin halin iya fada musu gaskiya."

Shehu ya kuma yi kira ga jam'iyyar Communist ta gayyaci shugabannin jam'iyyun siyasar Najeriya zuwa taronta na gaba don su koyi yadda China ke amfani da jam'iyyar don kawo cigaba a kasarsu.

Akwai abubuwa da dama da zamu iya koya daga China saboda siyasarmu na da banbanci.

Ku Daina Jiji da Kai, Ku Natsu Ku Kalli Wadanda Kuka Gada, Shawarin Shehu Sani Ga Gwamnoni

A bangare guda, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani ya ba da shawara kyauta ga dukkan gwamnonin Najeriya masu ci.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani wanda yake dan rajin kare hakkin bil-adama ne ya ce duk wani gwamnan da ke jin kansa tamkar sarki ya kamata sake tunani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel