Ku Daina Jiji da Kai, Ku Natsu Ku Kalli Wadanda Kuka Gada, Shawarin Shehu Sani Ga Gwamnoni

Ku Daina Jiji da Kai, Ku Natsu Ku Kalli Wadanda Kuka Gada, Shawarin Shehu Sani Ga Gwamnoni

  • Tsohon sanata kuma mai rajin kare hakkin bil-adama, Shehu Sani ya ba gwamnonin Najeriya shawari kyauta
  • Ya ce ya kamata duk wani gwamna ko da kuwa sau daya ne ya natsu ya yi tunanin makomarsa bayan ya sauka
  • Shehu Sani ya sha yin maganganu irin wadannan masu cike da bukatar mai da hankali da natsuwa ga 'yan siyasa

Najeriya - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani ya ba da shawara kyauta ga dukkan gwamnonin Najeriya masu ci.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani wanda yake dan rajin kare hakkin bil-adama ne ya ce duk wani gwamnan da ke jin kansa tamkar sarki ya kamata sake tunani.

A cewar Shehu Sani, gwamnonin da suka sauka daga mulki a baya da yadda suka kare ya ishi wadannan gwamnoni masu ci darasi.

Kara karanta wannan

Rushewar Ginin Kano: Tinubu ya Aike wa Ganduje Wasikar Jaje

Duk gwamnan da ke ji da mulki ya tsaya ya dubi wanda ya gada
Ya kamata gwamnoni suke duba makomarsu, da na gaba ake gane zurfin ruwa, inji Shehu Sani
Asali: Original

Ya kuma bukaci gwamnonin nan masu ci dake nuna isa a yanzu da su natsu su kirga adadin yawan abokan da suke dashi a halin yanzu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Shehu Sani:

"Ina fatan gwamnoni masu ci dake jin kansu tamkar sarakuna da su natsu su yi tunanin meye ya faru da wadanda suka gada, wadanda a baya su ke da mulki.
"Ya kamata gwamna ya tsaya ya kirga yawan abokai da masoyansa ya zuwa karshen lokacin da zai bar kujerar mulki."

Shehu na yawan magana kan masu mulki da kuma halayen da za su iya shiga nan da su sauka daga mulki.

Ya kasance tsohon sanata, kuma ya nemi takarar gwamna a zaben 2023 karkashin PDP amma ya rasa tikitin takara a zaben fidda gwani da aka yi a watannin da suka gabata.

Kara karanta wannan

Rudani: Bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaro ke dukan 'yan mata marayu a Saudiyya, an fara bincike

Shehu Sani ya fadi gaskiyar yadda ya samu fam din neman takarar Gwamnan Kaduna a PDP

A wani labarin, wani ‘danuwa a wajen Marigayi Umaru Musa Yar’Adua watau Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua ya na so ya yi takarar gwamna a jihar Katsina.

Daily Trust ta ce Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua ya karbi fam din shiga takara, ya na mai sa ran samun tikitin jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa.

Aminu Yar’Adua da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Yar’Adua, kakansu daya. Marigayi Yar’Adua ya yi gwamna a Katsina tsakanin 1999 da 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel