Rundunar Sojin Sama Ta Halaka Manyan Yan Ta’adda 3 a Zamfara
- Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a wani hari ta sama da suka kai a jihar Zamfara
- Dakarun Operation Hadarin Daji sun yi nasarar kashe wasu manyan yan bindiga uku da ake nema ido rufe
- 'Yan bindigar da aka kashe sun hada da Halilu Buzu, Yellow Kano, Alhaji Gana da kuma mayakansu sannan an tayar da sansanin boye kayayyakinsu
Zamfara - Hukumomin soji sun bayyana cewa rundunar Operation Hadarin Daji sun halaka manyan yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, Halilu Buzu, Yellow Kano, Alhaji Gana da sauransu bayan an kai masu hari ta sama a watan jiya, rahoton Vanguard.
An tattaro cewa harin ya yi sanadiyar halaka yan ta’adda da dama da kuma lalata wajen ajiyar kayayyakinsu a karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.
Yadda sojojin sama suka kai samamen
Majiyoyi sun ce harin saman ya gudana ne bayan bayanan sirri ya nuna cewa wani kasurgumin dan ta’adda, Halilu Buzu na Sububu a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara ya shirya taron sassafe tare da kwamandoji da wasu mayakansa a yankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton sirrin ya nuna wuri da ainahin sansanin ajiyar kayayyakinsa inda shi da mukarrabansa suke ajiye makamai, ababen hawa, babura da sauran abubuwan da suka sata.
Don haka sai jirgin NAF ya yunkura don kai farmaki wajen taron da kuma sansanin ajiyar tasu.
An lura da gagarumin wuta da ya tashi bayan harin da aka kai wajen ajiyar tasu, hakan ya nuna cewa wajen na dauke da wasu bama-bamai da abubuwan fashewa.
Hankalin mazauna yankin ya kwanta a yanzu
Majiyar ta ce:
“Kisan Halilu Buzu ya kamar an zare kaya ne ga mazauna Sububu, Anka (Bayan Daji) da yankin Bayan Ruwa a jihar Zamfara saboda addabarsu da kuma azabtar da mutanen da ya sace.
“Tuni rashinsa ya saukaka yawan garkuwa da mutane, satar dabbobi da sauran ayyukan ta’addanci a yankin.”
Hakazalika sojoji sun farmaki mabuyar kasurgumin dan ta’adda Alhaji Ganai a dajin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar 14 ga watan Nuwamban 2022, rahoton Leadership.
Hakan ya kasance ne bayan bangaren leken asiri sun kula tare da bibiyar ayyukan Alhaji Ganai da mayakansa a tsakanin wajen.
A wani labarin kuma, al'ummar jihar Zamfara sun yanke kauna bayan rundunar soji ta ayyana neman madugun dan bindiga Bello Turji ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng