Kasuwa ta Juya, Farashin Abinci ya Sauka War-was Jim Kadan Bayan Tsadar Hatsi

Kasuwa ta Juya, Farashin Abinci ya Sauka War-was Jim Kadan Bayan Tsadar Hatsi

  • Kayan amfanin gona sun rage daraja a makon nan, bayan tashin da suka yi a makon da ya shude
  • Shinkafa, masara, gero, waken suya da sauran hatsi duk sun rage tsada a kasuwanni a yanzu
  • Ana zargin masu ajiye kudi ne suka jawo farashi suka tashi da farko, kafin darajarsu tayi kasa

Nigeria - Kwanaki kadan bayan kayan abinci sun yi daraja sosai a kasuwa, sababbin rahotanni suna nuna farashin ya fara rugujewa sosai a halin yanzu.

Daily Trust tace farashin buhun kayan abinci kamar shinkafa, masara, waken suya, gero da sauran hatsi sun yi kasa a manyan kasuwannin da ake da su.

A kasuwar dawanau, buhun masara mai cin kilo 100 da aka saya a kan N26, 000 a makon jiya ya dawo N21, 000. An samu bambancin N5000 a duk buhu.

Kara karanta wannan

Kasuwar canji: Naira ta Bada Mamaki, Dala Tayi Mummunan Fadi, Ta Rasa Kusan N200

Babban buhun gero ya sauko daga N270, 000 zuwa N21, 000 a kasuwar da ke garin Kano. Waken suyan da aka saida a N37, 000 ya karye zuwa N31, 000.

Haka zalika rahoton ya nuna buhun gero ya koma N21, 000. a maimakon N26, 000 da aka rika saidawa a wannan babbar kasuwar hatsi da ke garin Kano.

Kasuwannin Taraba

A kasuwannin hatsin da ke Maihula, Kungana da Jatau a Taraba, masarar da aka saida tsakanin N20, 000 da N21, 000 a ta dawo N14,000 zuwa N15, 000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayan noma
Dalar shinkafa a Abuja Hoto: guardian.ng
Asali: Getty Images

A makon jiya an saida babban buhun shinkafa a kasuwannin jihar a N20, 000, yanzu da N18, 000 mutum zai samu buhu, haka farashin waken suya ya sauka.

Abubuwa sun ja baya a Kaduna

A garin Soba da ke jihar Kaduna, kasuwanni sun ja baya a makon nan. Shinkafar gida ta koma N19, 000 a maimakon N21, 000 da aka rika saida duk buhu.

Kara karanta wannan

Ba Zai Yiwu A Cigaba Da Sayar Da Litan Man Fetur N170 ga Lita Ba, Shugaban NNPC

Waken suya da aka yi ta sayen buhunsa a kan N35, 000 ya sauka da N6, 000. Manoma sun shaidawa jaridar cewa masara da sauran hatsi sun karye a yanzu.

Haka lamarin yake a kasuwannin da ke Nasarawa da Benuwai a tsakiyar Arewacin Najeriya.

Me ya jawo haka?

Ana zargin sanarwar canjin kudin da gwamnan CBN ya bada ne ya jawo masu kudi suka rika neman sayen amfanin gona, hakan ya sa kaya suka tashi da farko.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun yi mamakin yadda farashin kaya suka yi kasa a lokaci daya, bayan da farko manoma sun rika saida kayansu da daraja sosai.

Dala ta sauka a BDC

Rahotanni a baya sun nuna cewa Dalar da ake nema ido rufe a kwanakin baya ta zama abin gudu a kasuwannin canji sakamakon karyewar farashinta.

Mun fahimci cewa ‘Yan kasuwa sun yi asara a makon jiya. Farfadowar Naira a kasuwa ta sa ‘yan Canji sun guji sayen Daloli saboda za su iya karyewa.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng