Abuja, Katsina, Kano Da Wasu Jihohi 24 Wadanda Zasu Shiga Matsalar Abinci a 2023

Abuja, Katsina, Kano Da Wasu Jihohi 24 Wadanda Zasu Shiga Matsalar Abinci a 2023

Rahoton Cadre Harmonise (CH) ya gargaɗi babban birnin tarayya Abuja, jihar Legas da ƙarin wasu jihohi 25 a Najeriya cewa da yuwuwar su fusakanci matsanancin rashin abinci da kayan gina jiki a shekara mai zuwa.

The Nation tace jihohin da rahoton ya yi hasashe sun haɗa da, Abiya, Adamawa, Bauchi, Benuwai, Borno, Kuros Riba, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, da Katsina.

Sauran sune, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, da kuma jihar Zamfara.

A cewar rahoton 'yan Najeriya miliyan 25.3 ake hasashen zasu shiga matsalar rashin abinci a jihohi 26 tsakanin watan Yuni da Agusta, 2023.

Matsalar karancin abinci.
Abuja, Katsina, Kano Da Wasu Jihohi 24 Wadanda Zasu Shiga Matsalar Abinci a 2023 Hoto: @thenation
Asali: Twitter

Daga cikin jihohin dake sahun gaba da yawam waɗanda matsalar zata shafa akwai Borno mai mutane miliyan 1.4m, Yobe da miliyan 1.3m da kuma Adamawa mai miliyan ɗaya cif.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ba Tada Dan Takarar Gwamna A Akwa Ibom, Kotu Tace A Sake Zabe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya kuma bayyana cewa kusan 'yan Najeriya miliyan N17m ne ke fama da rashin abinci yanzu haka ciki harda 'yan gudun Hijira da kuma waɗanda aka maida gidajensu.

Haka nan rahoton yace mutane 41,000 waɗanda a halin yanzun suke fama da yunwa zasu shiga matsanancin yanayin rashin abinci daga cikin yan gudun Hijira 83,000 a jihohin Benuwai, Taraba da Kuros Riba.

A wannan lokacin da aka ɗiba, cin abinci zai ragu sakamakon raguwar magidanta, da kayan abinci da kuma hauhawar farashi? kayan abinci a kasuwanni.

Ƙungiyar kula da Abinci da noma ta majalisar ɗinkin duniya (FAO) da wasu ƙawayenta ne suka gudanar da wannan bincike karkashin jagorancin gwamnatin Najeriya ta hannun ma'aikatar noma da raya karkara.

Abubuwan da suka jawo rashin isasshen abinci

Rahoton ya ayyana rashin tsaro, ambaliyar ruwa, hauhawar farashin kayan abinci, tashin farashin kayan noma da faɗuwar darajar Naira a matsayin manyan abubuwan da suka jawo ƙalubalen.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Yace mutane kusan miliyan ɗaya ne zasu tsinci kansu cikin matsanancin rashin isasshen abinci ko abinda ya zarce haka muni daga watan Yuni zuwa Agusta, 2023.

Binciken ya ƙara nuna cewa a tsawon wannan lokacin, mafi yawan Magidanta a jihohin da ake hasashen abun zai fi ƙamari zasu fara fafutukar neman hanyar tanadar abubuwan buƙatunsu.

Wannan ba sabon abu bane a jihohin dake fama da matsalar ta'addanci kamar Borno, Adamawa da Yobe. Haka nan jihohin da ayyukan 'yan bindiga suka shafa, Katsina, Sokoto, Kaduna da Zamfara.

"A tsawon wannan lokaci waɗannan yankunan zasu koma amfani da dabarun ɓoye kayan bukatu kuma babu shakka hakan zai haddasa ƙaranci abinci har sai an ci gaba da ayyukan jin ƙan da ake yi yanzu."

Jakadan FAO a Najeriya, Fred Kafeero, a wurin gabatar da rahoton a Abuja, ya roki gwamnati a kowane mataki ta kutsa wannan lamari a kasafin kudi da sauran shirye-shiryenta ga al'umma.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abubakar A Kotu Kan Satar Burodi A Kaduna

Yace binciken CH karbaɓɓe ne saboda suna fitar da gamsasshe kuma amintaccen bayanai na gaskiya duba da hanyar maslaha da suke amfani da ita wajen tara bayanansu.

A ɓangarensa, babban Sakataren ma'aikatan noma da raya karkara, Dr Ernest Umakhihe, ya tabbatar da cewa gwamnati ta shirya tsaf wajen ɗaukar shawarin da suka fito daga rahoton da nufin daƙile lamarin a waɗannan jihohi.

FG ta haramta fitar da wasu kayayyaki daga Najeriya

A wani labarin kuma gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar kwastam ta haramta wa yan ƙasar fitar da wasu kayayyaki zuwa ƙasahen ƙetare

Tace duk wanda aka kama da yu kurin fitar da waɗannan kayayyaki ba bisa ƙa'ida to ya kuka da kansa domin zai fuskanci hukunci gwargwadon abinda ya aikata.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen kayayyakin guda Takwas, wanda ya haɗa da Masara, Katako, Ƙarafa da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262