Sojoji Sun Saki Sunaye Da Hotunan Shugabannin 'Yan Ta'adda 19 Da Ake Nema Ruwa A Jallo, Tare Da Tukwicin N5m
- Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta fitar da sunayen wasu gawurtattun shugaban yan ta'adda 19 da ta ke nema ruwa jallo saboda ayyukan ta'addanci
- Rundunar sojojin ta Najeriya ta bayyana cewa yan ta'addan sun dade suna adabar jihohin arewa maso gabas, arewa maso yamma, da arewa ta tsakiya
- Rundunar ta yi alkawarin bada tukwicin zunzurutun kudi Naira miliyan 5 ga duk dan Najeriya da ya bada bayanai da suka yi sanadin kama kowanne cikinsu
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta Najeriya, a ranar Litinin ta fitar da sunayen kwamandojin yan ta'adda 19 da ke adabar yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a kasar, rahoton Daily Trust.
Hedkwatar tsaron ta ce za ta ba'ada tukwicin Naira miliyan 5 ga duk wani dan Najeriya da ya bada bayanan yadda za a kama yan ta'addan, ta bukaci al'umma su tuntube ta a wannan lambar 09135904467.
Ta ce hakan ya zama wajibi ne domin cigaba da kawar da abokan gaban, inda ta kara da cewa hakan yunkuri ne na dawo da zaman lafiya gaba daya a kasar, rahoton LIB.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sunayen yan ta'addan da ake nema ruwa a jallo da Direkta na sashen watsa labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar sune:
Sunayen kwamandojin 'yan ta'adda 19 da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo
- Sani Dangote – Asalinsa: Kauyen Dumbarum . Karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
- Bello Turji Gudda – Asalinsa: Kauyen Fakai na Jihar Zamfara.
- Leko – Asalinsa: Kauyen Mozoj, Karamar Hukumar Mutazu ta jihar Katsina.
- Dogo Nahali – Asalinsa: Kauyen Yar Tsamiyar Jno. Karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
- Halilu Sububu – Asalinsa: Kauyen Sububu a karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara.
- Nagona – : Asalinsa: Kauyen Galadima a Isa Loa na jihar Sokoto.
- Nasanda – : Asalinsa, Kauyen Village a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
- Isiya Kwashen Garwa – Asalinsa: Kauyen Kamfanin Daudawa na karamar hukumar Faskari, Jihar Katsina.
- Ali Kachallaa da aka fi sani da Ali Kawaje – Asalinsa: Kauyen Kuyambara da ke karamar hukumar Danaadau Maru na jihar Zamfara.
- Abu Radde – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
- Dan-Da – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.
- Sani Gurgu – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina.
- Umaru Dan Najeriya – Asalinsa: Kauyen Rafi. Garin Mada a Gusaulaga.
- Nagala – Asalinsa: Karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
- Alhaji Ado Aliero – Asalinsa: Kauyen Yankuzo da ke karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara.
- Monere – Asalinsa: Kauyen Yantumaki , karamar hukumar Dan na jihar Katsina.
- Gwaska Dankarami – Asalinsa: Kauyen Shamushele da ke karamar hukumar Zuri na jihar Zamfara.
- Baleri – Asalinsa: Karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara.
- Mamudu Tainange – Asalinsa: Kauyen Varanda a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Najeriya Ta Zo Lamba 1 A Jerin Kasashen Duniya Da Aka fi Shan Wiwi: Buba Marwa Ya Tabbatar da Rahoton UN
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 60, Sun Kama Wasu Fiye da 90, DHQ
A wani rahoton, hedkwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana a ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba cewa, jami'an sojojin kasar sun yi ayyukan kakkabe 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Sanarwar da hedkwatar ta fitar ta bayyana cewa, akalla 'yan ta'adda 60 na Boko Haram/ISWAP jami'an sojoji suka hallaka, yayin da aka kama wasu 90 daga 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng