Najeriya Ta Zo Lamba 1 A Jerin Kasashen Duniya Da Aka fi Shan Wiwi: Buba Marwa Ya Tabbatar da Rahoton UN

Najeriya Ta Zo Lamba 1 A Jerin Kasashen Duniya Da Aka fi Shan Wiwi: Buba Marwa Ya Tabbatar da Rahoton UN

  • Hukumar NDLEA ta bayyana sakamakon binciken da majalisar dinkin duniya ta gudanar kan Wi-wi
  • Najeriya ta yiwa kasashe irinsu Jamaica, Mexico, Kolumbia da Portugal zarra; itace ta 1 wajen shan Wi-wi
  • Buba Marwa ya bayyana gagarumin nasarar da hukumar ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata

Legas - Shugaban hukumar hana ta'amuni da muggan kwayoyi NDLEA, Muhammad Buba Marwa, ya bayyana cewa Najeriya ce kasa ta daya a jern kasashen duniya da ake shan wi-wi.

Marwa ya bayyana cewa akalla yan Najeriya milyan 10.6 ke shan ganyen na Wi-wi.

Ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na kiwon lafiya kwakwalwa da jaridar Vanguard tare da hadin kan 9Mobile da GTBank suka shirya, rahoton Vanguard.

Ndlea
Najeriya Ta Zo Lamba 1 A Jerin Kasashen Duniya Da Aka fi Shan Ganye: Buba Marwa Ya Tabbatar da Rahoton UN
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

A cewarsa, Najeriya ba ta san ta'amuni da ganyen Wi-wi ya yi muni ba sai lokacin da majalisar dinkin duniya ta gudanar da bincike a 2018.

A cewarsa:

"Gabanin rahoton, bamu da cikakken bayanin masu ta'amuni da kwayoyi a Najeriya. Binciken ya kara mana haske cewa kawo 2018 a Najeriya, kashi 14.4% na yan kasar yan kwaya ne."
"Sauran kasashen duniya kashi 5.5% ke ta'amuni, amma Najeriya ya ninka su kusan sau uku 14.4%. Ko shakka babu Najeriya na da matsalar kwaya."
"Abu na biyu, binciken ya kara haske kan ire-iren mayan mayen da ake sha a sassan Najeriya daban-daban."
"Mafi tada hankali shine cewa yan Najeriya milyan 10.6 ke shan Wiwi. Masu shan Wiw a Najeriya sun kasashe irin Portugal da UAE yawa."

Nasarorin da muka samu

Marwa wanda ya samu wakilcin Zonal Kwamanda na Legas, Dr. Segun Oke, ya bayyana irin nasarorin da suka samu cikin shekaru biyu da suka gabata

Kara karanta wannan

N165bn sun dawo: CBN ya ce sabon kudi ya fara yawo, sabon batu mai muhimmanci ya fito

Yace:

"Cikin watanni 22, hukumar ta damke yan kwaya 20,000 kuma an gurfanar da 3,111 a kotu. Mun kwace 5.5 million kg na kwayoyi, mun kona gonakin wiwi na hakta 900 kuma mun bankado wajen hada kankarar methamphetamine."

Ya bada tabbacin cewa a shekara mai zuwa, gyaran fuskar da aka yiwa dokar NDLEA zai taimaka wajen turmusa yan kwaya kurkuku na tsawon shekaru kuma ba zasu iya biyan tara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel