Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 60, Sun Kama Wasu Fiye da 90, DHQ

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 60, Sun Kama Wasu Fiye da 90, DHQ

  • Hedkwatar tsari ta bayyana ayyukan da jamia'an sojojin Najeriya suka aiwatar a yankuna daban-daban na kasar nan
  • Hakazalika, an kama wasu 'yan ta'adda Boko Haram, wasu da dama sun mika kai ga jami'an sojin kasar
  • Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda, hakan kuma na karya kashin bayan ta'addanci

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana a ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba cewa, jami'an sojojin kasar sun yi ayyukan kakkabe 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashi.

Sanarwar da hedkwatar ta fitar ta bayyana cewa, akalla 'yan ta'adda 60 na Boko Haram/ISWAP jami'an sojoji suka hallaka, yayin da aka kama wasu 90 daga 'yan ta'addan.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram da yawa a Borno
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 60, sun kama wasu fiye da 90, DHQ | Hoto: tribuneonline.com
Asali: UGC

Hakazalika, ta ce akwai sama da 'yan ta'adda 145 da suka mika kansu ga jami'an tsaro ciki har da mata da yara kanana a zagayen shiyyoyi shida na Najeriya, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Arewa

Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan yada labarai na gidan tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami a taron bayyana nasarorin jami'an tsaro na kowane mako biyu da aka a makon nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa, ayyukan da kuma nasarar da aka samu sun samu ne ta dalilin kara jajirewar jami'an tsaron da ke yakar ta'addanci a fadin kasar nan.

An kwato albarkatun man fetur da 'yan ta'adda suka sace a yankin Neja Delta

A bangare guda, ya yi tsokaci game da kayayyakin da aka kwato daga hannun 'yan ta'adda a yankin Kudancin kasar nan, musamman masu alaka da man fetur

Ya kara da cewa, a aikin da jami'an tsaro suka yi cikin mako biyu, sun kwato albarkatun man fetur da darajarsu ta kai N2,435,021,343.94 a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun gamu da ajali, jami'an tsaro sun ragargaje su a wata jiha

Cikakkiyar sanarwar da muka samo daga shafin Facebook na hedkwatar tsaro ya bayyana adadin kayayyakin da jami'an tsaron suka kwato, har da karin bayani.

Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Uku a Jihar Anambra

A wani labarin, hadin gwiwar jami'an tsaro a jihar Anambra sun yi bata-kashi da wasu tsagerun 'yan bindiga, sun hallaka uku.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba a Umunze, karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar ta Anambra.

Rahoton da muke samo daga jaridar The Nation ya bayyana cewa, an samu layu da guraye a jikinsu, musamman a kafa, wuya, kugu da hannaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel