Babu Yajin-aiki, ASUU Sun Jero Matakai 2 da Za Su Dauka a Kan Biyansu Rabin Albashi

Babu Yajin-aiki, ASUU Sun Jero Matakai 2 da Za Su Dauka a Kan Biyansu Rabin Albashi

  • ‘Yan Kungiyar ASUU za su shiga zanga-zanga da nufin nunawa gwamnatin tarayya rashin jin dadinsu
  • Gwamnati ta biya malaman jami’o'i albashin rabin wata a Oktoba saboda suna yajin-aiki, ba su shiga ofis ba
  • ASUU tace za tayi zanga-zanga, kuma a tsaida karatu a jami’o’i saboda zaftare masu albashinsu da aka yi

Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya tana shirin yin zanga-zangar lumuna a fadin Najeriya domin nunawa gwamnatin kasar fushinta.

Punch ta kawo rahoton da ya nuna cewa malaman jami’an za suyi zanga-zanga na kwana guda saboda rashin hana su albashi da gwamnatin tarayya tayi.

Gwamnatin tarayya ta dauki tsarin ‘babu aiki-babu albashi’ ga malaman da suka shiga yajin-aiki. Wannan mataki ya fusata 'ya 'yan kungiyar ASUU.

Za a gudanar da wannan zanga-zanga ne a jami’o’in gwamnati da ke jihohin kasar nan. Ana sa ran a ga malaman da ke cikin kungiyar sun hau tituna.

Kara karanta wannan

Rabin Albashi: Badaru Ya Bayyana Kokarin da Suke Tsakanin ASUU da FG

Babu shiga aji a ranar

Hakan yana nufin a ranar da za ayi wannan zanga-zanga ta lumuna, ba za a koyar da dalibai ba. Babu malamin jami’ar da zai shiga aji domin bada darasi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani ‘dan majalisar koli watau NEC ta kungiyar ASUU, ya shaidawa Punch wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a ranar Lahadin da ta wuce.

Zanga-zanga a Legas
Wasu masu zanga-zanga a Legas Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Malamin jami’ar yake cewa kowace makaranta za ta tsaida ranar da za tayi na ta zanga-zangar, ba a lokaci daya za a kaure da zanga-zangar a Najeriya ba.

"Za muyi zanga-zanga. Kowani reshe zai zabi ranar da za iyi, ya kamata gwamnati ta fahimci mu ba ma’aikatan wucin-gadi ba ne.”

- Wani 'Dan ASUU

LASU sun zabi ranar Talata

Shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar Legas, Dr. Dele Ashir, ya tabbatar da cewa za suyi na su zanga-zangar ne a ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

Wasikar da kungiyar ASUU ta fitar ya nuna cewa ana gayyatar duk wasu masu ruwa da tsaki zuwa wajen zanga-zangar a dakin taro na Julius Berger a gobe.

Jaridar Tribune ta iya tabbatar da wannan rahoto a yammacin Lahadin nan.

Har zuwa yanzu shugaban ASUU na kasa baki daya watau Farfesa Emmanuel Osodeke bai yi bayanin matsayar da uwar kungiya ta dauka ba tukuna.

ASUU v El-Rufai

Kwanakin baya ne aka ji labari Kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta na rigima da Gwamnan Kaduna, Nasie El-Rufai.

ASUU ta yi kira ga shugabannin jami’ar ABU Zaria da su karbe digirorin Nasir El-Rufai saboda ya karbe filin jami'ar, yana mai ikirarin na gwamnati ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel