Kaiwa Magoya Bayan Atiku Hari: Yan Sanda Sun Kama Mutum 12
- Yan sandan jihar Ribas sun cika hannu da wasu mutane 12 da ake zargin suna cikin wadanda suka kai hari ga magoya bayan Atiku Abubakar
- Wasu yan baranda sun farmaki wasu mutane uku da ke aikin manna fastocin dan takarar shugaban kasar na PDP da adduna a yankub Omuma a ranar Lahadi
- Kwamishinan yan sandan Ribas, Okon Effiong, ya yi kira ga jam'iyyun siyasa a kan su ja kunnen magoya bayansu don ba za su taba lamuntan karya doka ba
Rivers - Rundunar yan sandan Ribas ta sanar da kama mutum 12 da ake zargin suna da hannu wajen kaiwa magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, hari a jihar, Nigerian Tribune ta rahoto.
An tattaro cewa an farmaki wasu mutum uku da adduna a ranar Lahadi yayin da suke tsaka da manna hotunan kamfen din Atiku a yankin Eberi-Omuma da ke karamar hukumar Omuma ta jihar.
Za a gurfanar da su gaban kotu da zaran an kammala bincike
Kwamishinan yan sandan jihar Ribas, Okon Effiong, ya sanar da kamun wadanda ake zargin a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, yayin wata ganawa da jam’iyyun siyasa da yan takararsu a Port Harcourt, babban bienin jihar Ribas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
CP Effiong ya bayyana cewa wadanda ake zargin su 12 suna amsa tambayoyi kuma za a gurfanar da wadanda aka kama da laifi a tsakaninsu a gaban kotu.
Ya kuma gargadi yan siyasa cewa ba za a lamunci dabar siyasa ko tayar da rikici ba a jihar Ribas yayin da ake yakin neman zaben 2023.
Bugu da kari, ya yi gargadi kan duk wani nau’I na rikici da tarwatsa gangamin siyasa ko hotunan siyasa yayin kamfen din zaben 2023.
Ya fada ma yan takara da shugabannin jam’iyyun siyasa da suka halarci taron da su shawarci magoya bayansu da kada su kasa kansu a kowani rikici domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri daidai da doka.
Kwamishinan ya bayar da tabbacin cewa yan sanda za su zamo a tsakiya wajen gudanar da aikinsu kafin, lokaci da kuma bayan zabe mai zuwa.
Ya bukaci jam’iyyun siyasa da yan takararsu da su gabatar da tsare-tsaren kamfen dinsu don yan sanda su samu damar shirya masu tsaron da yakamata.
Ya umurce su bayar da hadin kai don yin zabe cikin lumana, yana mai gargadin cewa ba za a lamunci duk wani nau’I na tarwatsa yakin neman zabe a jihar ba yana mai umurtansu da su shawarci mabiyansu da su guji rikicin siyasa, rahoton PM News.
Yan baranda sun farmaki magoya bayan Atiku
Mun dai ji a baya cewa an bindige mutum daya a harin da aka kaiwa magoyan bayan dan takarar shugaban kasar na PDP.
An tattaro cewa matasa wadanda yawansu ya haura 30 ne suka farma mutanen da adduna a yankin na Omuma.
Asali: Legit.ng