'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malaman Addini Biyu a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malaman Addini Biyu a Jihar Filato

  • 'Yan bindiga sun yi Garkuwa da wasu manyan Malaman Kirista biyu a Mararrabar Jema'a, Jos ta kudu jihar Filato
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tare Malaman da misalin karfe 8:00 na daren Laraba yayin da suke hanyar zuwa Jos
  • Wani mamban iyalai ya bayyana cewa masu garkuwa sun nemi a biya miliyan N10m a matsayin kuɗin fansa

Jos, Plateau - Rahotanni sun nuna cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da Malamai biyu a yankin Mararrabar Jema'a, ƙaramar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

Lamarin ya faru da Malaman ne yayin da suke kan hanya daga Mangu zuwa Jos ba zato maharan suka tarbe su sannan suka tafi da su da misalin ƙarfe 8:00 na daren Laraba (jiya).

Harin yan bindiga a Jos.
'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malaman Addini Biyu a Jihar Filato Hoto: punchng
Asali: Twitter

Vanguard ta tattaro cewa ɗaya daga cikin Malaman da aka sace, Fasto Nuhu Bakwa, mazuanin Abuja, mahaifinsa ya rasu a ƙauyen Farin Ƙasa, Mangu Halle a karamar hukumar Magu dake jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: 'Yan Daba Sun Kaiwa Ayarin Ado Doguwa Hari a Kano, Ya Magantu Kan Masu Hannu

An ce a hanyarsu ta komawa gida domin shirya masa Jana'iza tare da iyalai da abokinsa, wanda shi ma Malamin Addinin kirista ne, lamarin ya rutsa da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har zuwa yanzun da muke haɗa muku wannan rahoton, kakakin hukumar 'yan sandan Filato, DSP Alfred Alabo, bai ce komai ba game da faruwar harin.

Amma wani mamban gidan Malamin ya tabbatar da kai harin, inda yace:

"A ranar Talata mahaifin Fasto Nuhu Bakwa ya mutu a Farin Ƙasa, yankin Magu Halle. Ya baro Abuja inda yake zaune zuwa ƙauyen domin fara shirye-shiryen Jana'iza."
"Jiya (Laraba) ya kama hanyar zuwa Jos lokacin da suka isa Mararrbar Jema'a da matarsa, yaransu da kuma wani Fasto Abokinsa ba zato aka tsayar da su. Nan aka tafi da Malaman biyu aka bar matar da yaranta."

Shin maharan sun nemi kuɗin fansa?

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Mutumin ya ƙara da cewa masu garkuwan da suka sace Malaman sun tuntuɓi 'yan uwa kuma sun nemi a biya miliyan N10m kafin su sako su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

"Na fahimci cewa masu garkuwan sun kira waya, sun bukaci a tattara musu miliyan N10m a matsayin kuɗin fansa. Harin ya faru ne a tsakanin karfe 8:00 zuwa 9:00 na dare."

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu 'yan bindiga sama 50 sun sheka barzahu yayin da suka yi yunkurin kai hari a jihar Neja

Rahotannin da muka tattara sun nuna cewa yan bindiga sun kai hari wata Ruga a yankin ƙaramar hukumar Shiroro, bisa sa'a mutane suna sanar da jami'an tsaro.

Bayan sace shanu sama da 200 a Rugar, da yawan yan bindigan sun gamu da ajalinsu ne yayin da haɗin guiwar jami'an tsaro suka tarbe su aka gwabza artabu.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan Bindiga Sama da 50 Sun Bakunci Lahira a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262