Rikicin APC Kano: Yan Daba Sun Kaiwa Ayarin Ado Doguwa Hari, Ya Magantu

Rikicin APC Kano: Yan Daba Sun Kaiwa Ayarin Ado Doguwa Hari, Ya Magantu

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin tarayya, Alhassan Doguwa, yace wasu yan daba sun kai wa ayarinsa hari
  • Doguwa yace ya yi matuƙar mamakin harin da aka kai masa duk da an sulhunta tsakaninsa da Sulen Garo
  • Yan sanda sun ce basu da labarin abinda ya auku amma Doguwa yace an jikkata magoya bayansa

Kano - Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, yace wasu mutane da ya ayyana da 'yan daban siyasa sun farmaki tawagarsa a kofar Filin Jirgin Malam Aminu Kano.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Doguwa ya bayyana cewa lokacin da aka kai masa hari, tsagerun sun yi kaca-kaca da Motarsa guda ɗaya.

Alhassan Ado Doguwa.
Rikicin APC Kano: Yan Daba Sun Kaiwa Ayarin Ado Doguwa Hari, Ya Magantu Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Haka zalika a wani harin na ɗaban, ɗan majalisar yace maharan sun jikkata magoya bayansa kuma suka yi awon gaba da Mota ɗaya a Gandun Albasa, gefen gidan Bashir Tofa.

Kara karanta wannan

Gwamna Lalong Ya Shigar Da Ali Nuhu, Duniyar Kannywood Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima

Mista Doguwa yace ya yi matuƙar mamakin kai masa wannan harin guda biyu saboda ya shirya da Garo bayan tsoma bakin ɗan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu da gwamna Ganduje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An yi kaca-kaca da Hotunana a kwaryar birnin Kano, an farmaki ayarin motoci na a ƙofar Filin jirgin Kano, kuma an ɓatamun mota, na san masu hannu a lamarin."

- A cewar Doguwa a wani Radiyo na jihar Kano yayin da yake kira da masoyansa su kwantar da hankulansu.

Yadda aka kwantar da magoya bayana a Asibiti - Doguwa

Ya ƙara da cewa an farmaki wasu daga cikin magoya bayansa da Adduna, uku daga ciki yanzu haka suna kwance a Asibiti yayin da aka sallami wasu uku.

"An kaiwa wata mota hari mai ɗauke da mutanen mazaɓata a kusa da gidan Baahir Tofa. Yayin harin yan daban sun sari da yawansu da Adda, uku na kwance a Asibiti, an sallami wasu, motar kuma sun saceta."

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Shiga Tsakanin Doguwa da Garo, Yayi Musu Sasanci

Legit.ng Hausa ta rahoto Doguwa na cewa ya yafe wa duk masu hannu a kai masa harin kuma ya nemi afuwar Ganduje, shugabannin APC da mambobi waɗanda watakila basu ji daɗin rigimarsa da Garo ba.

Sai dai da aka nemi jin ta bakin kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, yace har yanzun hukumarsu bata samu labarin lamarin ba.

Gwamnan Bauchi Ya Fusata da Atiku Abubakar, Ya Aike Masa da Sako Mai Zafi

A wani labarin kuma wata sabuwar Rigima ta ɓullo a jam'iyyar PDP yayin da aka hangi Gwamnan Bauchi ya aike da wasika ga Ayu

Gwamna Bala Muhammed, ya nuna fushinsa ƙarara da yadda aka maida shi saniyar ware a kwamitin kamfen Atiku na zaɓen 2023.

A wasikar gwamnan ya koka kan yadda Atiku ya ja wasu mutane daga Bauchi yake mara musu baya su na cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel